Zulum Zai Gina Ƙauyuka Uku Don Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijira 20,000


Daga Mujtaba Gali

Gwamnamn jihar Bornon Babagana Umara Zulum ya bayyana shirin sake gina wasu ƙauyuka uku domin sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar da mayaƙan Boko Haram suka raba da muhallansu.


Fiye da mutum 20,000 ne boko haram ta rana da muhallansu a jihohin Borno da Yobe da adamawa, waɗanda wasunsu ke zaune a makwabtan ƙasashen Nijar da kamaru da Chadi.


A wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce tun shekarar 2014 ne mayaƙan Boko Haram ta raba mutanen da muhallansu.


Zulum ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da kwamitin maido da ‘yan gudun hijirar da ke ƙasashen waje a Abuja babban birnin ƙasar.


Gwaman Zulum shi ne mataimakin kwamitin shugaban ƙasa na maido da ‘yan gudun hijirar ƙasar da ke zaune a ƙasashen waje , tare da sauya tunanin mutanen da da Boko Haram ta sako.


Inda mataimakin shugaban ƙasa farfesa Yemi Osinbajo ke zaman shugaban kwamitin.


Gwamna Zulum ya ce shugaba Buhari ya amince da bai wa kwamitin naira biliyan 15, yayin da gwamnatin jihar Borno ke shirin sake gina ƙauyuka uku don tsugunar da ‘yan gudun hijirar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: