“Zan yi amfani da mukami na wajen raya yankunan Karkara -Danlami Kurfi

Daga Aliyu Dangida
Hon Danlami Muhammad Kurfi yayi alkawarin yi amfani da damar sa a karkashin sabon ofishinsa don samarwa yankunan Karkara duk wani abu da kamata don inganta rayuwarsu.

Hon. Kurfi yayi wannan bayanin ne a lokacin da ya gayyaci shugabannin jam’iyyar APC na mazabarsa ta Barkiya da ke karamar hukumar Kurfi, domin tattauna wasu muhimman al’amura da suka shafi APC na cikin gida.

A satin da ya gabata ne, Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya amince da nadin Hon. Danlami Muhammad Kurfi a matsayin mukamin Shugaban Hukumar kula da samar da wutar lantarki a Karkara (REA) ta Najeriya.

Kurfi ya bayyana irin yadda aka bar yankunan karkara a baya wajen samun ababen more rayuwa, ya kara da cewa shi yasa ma ake samun masu garkuwa da mutane a cikinsu.

Hon Danlami ya godewa Shugaba Muhammadu Buhari akan damar da ya bashi, yace “In Sha Allahu zan yi amfani da wannan damar a karkashin Ofishina don samarwa yankunan karkara, duk wani abu da dace domin inganta rayuwarsu”.

Shugaban REA yace ko babu komai dama ni daga karkara na fito kuma na san matsalolinta don haka zan yi abinda ya dace don samar masu abubuwan more rayuwarsu.

Hon Danlami ya jajanta game da matsalar tsaro da yace a satin da ya gabata ya samu labarin masu garkuwa da mutane sun shiga garin Barkiya da wasu Unguwanni makwabta, inda yace, abinda ke gabanmu a halin yanzu shine addu’a, saboda ba magana bace ta wata jam’iyya, al’amari ne da ke bukatar sa ido da addu’a.

A karshe Danlami Kurfi ya kara tabbatar wa ‘Yan uwansa na mazabar Barkiya a ƙarƙashin jagorancin shuwagabannin Jam’iyyar APC na mazabar Barkiya cewa duk wani tallafi ko wane iri ne da zai samar da tsaro a yankin a shirye yake dama yanayi.

Shugaban jam’iyar APC na mazabar Barkiya yayi godiya da irin gudummawar da Hon. Danlami Kurfi yake basu a matsayinsu na ‘Ya’yan jam’iyyar APC, kuma ya ci alwashin jajircewa domin samar da kyakkyawan hadin kai a tsakanin’ya’yan jam’iyyar.

Daga karshe tsohon Kansilan riko na mazabar Barkiya yayi karin haske akan ire-iren ayyukan alkhairi da Danlami Kurfi yake yi masu, sun yi godiya tare da taya shi murna bisa wannan babban mukami da ya samu, inda yayi masa fatan alkhairi da Allah ya bashi iKon sauke nauyin da aka dora masa.

An gudanar da taron na sada zumunci ga ‘yan mazabar ta Barkiya a Dakin taro na HAYATT REGENCY SUITE Katsina, mallakar Hon. Danlami Kurfi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: