Zamu Farfaɗo Da Borno Ta Ci Gaba Da Zama Jihar Da Ke Samar Da Kayayyaki – Obi

Daga MGM

Dan takarar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar Labour Peter Obi, ya yi alƙawarun farfaɗo da Jihar Borno ta zama cikin jihohi masu samar da abubuwa ta zama cikin waɗanda Najeriya ke alfahari da su, idan aka zaɓe shi ya zama shugaban ƙasa.

Obi ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da wasu ɗalibai da matasa a wani taron da ya yi da jama’ai kafin ya fara gangamin neman zaɓe a Maiduguri.

Ya ce yana fatan sauya Najeriya zuwa yanayi mai kyau, inda zai tabbatar da adalci da daidaito da kuma samar da ayyukan more rayuwa, kuma su ne za su zama manyan abubuwan da na sa a gaba.

“Borno ta fi girman Belgium da Netherlands da Poland da kuma Isra’ila.

Muna tabbatar muka rashawa ba za ta samu wurin zama ba kazali rashin tsaro da yawan yajin aikin ASUU idan Obi ya zama shugaban ƙasa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: