Zaben 2023: NNPP Ta Zargi INEC Da Yi Mata Rufa Rufa

Daga Mujtaba Gali

Jam`iyyar adawa ta NNPP a Najeriya, ta nuna damuwa game da kin amincewar da hukumar zabe ta yi da wasu sunayen da ta gabatar mata domin maye gurbin wasu daga cikin `yan takararta da suka janye.

Jam`iyyar ta ce ta kai maganar gaban alkali, kuma sau biyu kotu tana ba ta gaskiya, amma hukumar zaben ta ci gaba da yin turjiya.

NNPP, ta ce ta bi dukkan ka’idojin da doka ta shimfida wajen mika sunayen ‘yan takararta na mukamai daban-daban ciki har da kujerar sanatan Kano ta tsakiya, wadda tsohon gwamnan jihar sanata Ibrahim Shekarau, ya janye bayan ficewarsa daga jam’iyyar.

To amma, jam’iyyar ta fara zargin hukumar zabe na mata wasa da hankali har ma ta fara zargin ko akwai wata rufa-rufa da hukumar zaben ke mata.

Injiniya Buba Galadima, jigo ne a jam’iyyar ta NNPP, ya shaida wa BBC cewa, su babban abin da ya dame su shi ne ko akwai wata jikakkiya tsakaninsu da hukumar zabe wadda ba su sani ba.

Ya ce, “ Duk dan Najeriya ya sani cewa Malam Ibrahim Shekarau, ya bar jam’iyyar NNPP, mun rubuta wa INEC cewa tun da Shekarau ya bar mu a bamu ranar da zamu sake zaben fitar da wani dan takarar da zai maye gurbin Shekarau.”

To amma sai INEC, ta rubuto cewa bata yarda ba, mu kuma muka fitar da dan takara muka aika musu amma suka ce ba su yarda ba,” inji shi.

Buba Galadima, ya ce daga nan suka garzaya zuwa kotu, kotu kuwa ta ce suna da gaskiya.

Ya ce, ‘’ Daga nan ne sai INEC, ta ce bata yarda ba ta daukaka kara, kotu ta gaba kuwa ta ce dole a kyale jam’iyyar da ya bari ta fitar da wani dan takara, sai suka ce sai sun sake daukaka kara zuwa kotun koli.”

Buba Galadima, ya ce ‘’ Wai shin mene ne ma bukatar INEC?”.

Bayan kujerar dan takarar sanata ta Kano ta tsakiya, akwai wasu kujerun kamar ta dan takarar sanata a jam’iyyar a Taraba ta Kudu Murtala Garba, wadanda a har yanzu hukumar zabe bata karbesu ba.

To sai dai kuma hukumar zaben ta ce bata da wata manufa game da jinkirin da ta ke yi wajen karbar sunayen masu takarar, face bukatar abi doka.

Wani babban lauyan a hukumar zaben, Tanimu Muhammad, ya shaida wa BBC cewa, ita hukumar zabe babu abin da take bukata illa kawai abi doka.

Ya ce,’’ Jam’iyyar NNPP ce ta fara gurfanar da mu gaban kotu, kuma ita kara a kan batun zabe karace da zata iya zuwa har kotun koli, shi ya sa muka tafi can don muna son sanin abin da ya kawo rikici tsakaninmu da ‘ya’yan jam’iyyar.”

Babban lauyan ya ce abin da suke nema su yi ya sabawa jadawalin da muka bayar.

Baya ga jam’iyyar NNPP, akwai wasu jam’iyyun da dama wadanda ke da irin wadannan korafi ko bukatar sauya sunayen da suke so su maye gurbin wasu ‘yan takara da suka janye, da suma suka zuba ido don ganin yadda zata kaya tsakanin hukumar zaben ta kasa da kuma jam’iyyar NNPP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: