Zaɓaɓɓen Gwamnan Zamfara da ‘Yan Majalisar Jihar Sun Amshi Takardar Shedar Samun Nasarar Zaben
Daga Hussaini Ibrahim
Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal da mataimakinsa, Mallam-Mani Mallam-Muni sun karbi takardar shaidar cin zabe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar, INEC, a babban birnin jihar Gusau.
Hukumar ta kuma mika takardar shaidar lashe zaben ga zababbun ‘yan majalisar dokokin Jiha 24, wadanda suka kunshi mambobi 17 daga jam’iyyar PDP, da bakwai daga jam’iyyar APC.
Sai dai zaɓaɓɓen Gwamnan, ya yi amfani da wannan damar wajen mika godiyarsa ga wadanda suka zabe su bisa jajircewar da suka yi wajen gudanar da zabe, ya kuma ba su tabbacin cewa kokarin da suke yi ba zai kasance a banza ba domin “gwamnatina za ta kawo sauye-sauye masu kyau da dora Jihar kan turbar ci gaban da ta dace”.
Daga nan sai ya bukaci jama’a da su yi amfani da watan Ramadan mai alfarma wajen yi wa gwamnatin da ke tafe addu’a don samun nasarar kawo ci gaban da ake bukata a jihar.
Lawal ya kuma godewa jama’a da jam’iyyar PDP da abokan arziki da suka ba shi damar lashe zaben gwamna a jihar.
Kwamishinan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, mai kula da Jihohin Kebbi, Sokoto da Zamfara, Farfesa Muhammad Kalla ya mika takardar shaidar cin zabe ga Zababben Gwamna Dauda Lawal da Mataimakin Malam- Mani Mallam-Muni.
Yayin da Kwamishinan Zabe na Jihar Zamfara, Babura Ahmed ya gabatar da takardar shaidar lashe zaben ga zababbun mambobi ‘yan majakisun 24 da cikin jihar ta Zamfara.