‘Yan Matan Sifaniya Sun Lashe Kofin Duniya
Daga Mujtaba Gali
Tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Sifaniya ta lashe gasar Kofin Duniya bayan doke Ingila a wasan ƙarshe na gasar ta 2023 da aka buga a Ausraliya.
Carmona ce ta ci ƙwallo ɗaya tilo a minti na 29 bayan ta ɗaɗa ta daga ɓangaren hagu da ƙafarta ta hagu.
Wannan ne karon farko da Sifaniya ta lashe gasar.