Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Dalibai a Jami’ar Dake Nasarawa


Labarai


Miyagun yan bindiga sun kai hari yankin jami’ar tarayya dake Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, inda suka yi garkuwa da wasu ɗalibai.


Hukumar jami’ar ta tabbar da sace ɗalibanta akalla hudu, ta kuma jajantawa iyalan waɗan da lamarin ya shafa tare da alƙawarin ceto yayansu.


Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Abdul Rahman, ya ziyarci Hedkwatar yan sanda, kuma ya sanar da kwamishina halin da ake ciki.


Nasarawa – Yan bindiga sun sace wasu daga cikin ɗaliban jami’ar tarayya dake Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa, a kusa da ɗakunan kwanan su.


A cewar wata majiya da Daily Trust ta rahoto, an sace ɗaliban ne a yankin da jami’arsu take wato Maraba.


Kakakin jami’ar, Abubakar Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa ɗalibai hudu ne maharan suka yi awon gaba da su.


Ya ƙara da cewa yan bindigan sun farmaki yankin jami’ar da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Alhamis, inda suka tasa ɗaliban zuwa wani wuri da ba’a gano ba.


Yace: “Mataimakin shugaban jami’ar (VC), Farfesa Shehu Abdul Rahman, a madadin jami’a ya nuna tsantsar damuwarsa tare da yin Allah wadai da lamarin, kuma ya bukaci a gaggauta sako ɗaliban da aka sace.”


Wannan barazana ce ga ilimi a Najeriya – VC
VC ya ƙara da cewa garkuwa da ɗalibai na ɗaya daga cikin abubuwan dake zama barzana ga ilimi a jihar Nasarawa, da kuma Najeriya baki ɗaya.


Yayin da yake jajantawa iyalan ɗaliban da aka sace, Farfesa Rahman, ya tabbatar musu da cewa yanzu haka ana cigaba da ɗaukar matakai domin ceto ɗaliban cikin sauri.

“Mataimakin shugaban jami’ar, wanda tuni ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, ya garzaya Hedkwatar yan sanda ta jiha, inda ya sanar da kwamishina abin da ya faru a hukumance.”


Me ya kamata ɗalibai su yi? Farfesa Rahman ya roki daliban jami’ar su maida hankali matuka kan abinda ya shafi tsaro, kuma ya bukaci su kwantar da hankulansu, su cigaba da harkokinsu.


Bugu da ƙari, yace hukumar jami’a ta kara daukar wasu matakai domin tabbatar da tsaro a ciki da wajen makaranta.


A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun yi mummunar ɓarna a babbar Sakateriyar jam’iyyar PDP Wasu yan bindiga ɗauke da muggan makamai da ake zargin yan daban siyasa ne sun farmaki sakatariyar PDP reshen jihar Ekiti.


Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi raga-raga da kujeru, sun lalata fayil-fayin, sannan kuma suka farfasa gilasan kofofi da tagogi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: