Yan Bindiga Sun Zamo Matsayin Yan Ta’adda: Gwamnati


Daga Bangaren Labaran Hausa


Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta amince da alanta ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.


Wannan na zuwa ne yayin da kiraye-kiraye suka yi yawa kan bukatar daukar mataki kan ‘yan ta’adda musamman a Arewa.


A baya dama kotu ta ba da umarnin gwamnati ta amince da wannan bukata, wanda yanzu dai da alamu ya tabbata.


Abuja – Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana aikin ‘yan bindiga a matsayin aikin ta’addanci a hukumance, kamar yadda FIJ ta tattaro.


Abubakar Malami, SAN, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyana a shirin ‘Barka da Hantsi’ na gidan Talabijin na Najeriya (NTA) a ranar Talata.


Ya ce ofishinsa na aiki don duba hukuncin da kotu ta yanke wanda ya umarci gwamnati ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.


A ranar Laraba, FIJ ta samu takardar, inda Malami ya sanya hannu a cikinsu.


A ranar 26 ga Nuwamba, 2021, Mai shari’a Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya amince da bukatar da gwamnatin tarayya na neman alanta ‘yan bindiga da ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: