‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Amarya Da Ango a Birnin Katsina

Daga BBC Hausa

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu sabbin ma’aurata bayan kashe jami’an sa-kai biyu a wani hari da suka kai unguwar Shola da ke birnin Katsina.

A cewar mazauna unguwar ‘yan bindigar sun far mu su ne da misalin ɗaya da minti ashirin da biyar na dare, kuma sun shafe sa’a guda su na harbe-harbe.

Sun shaida cewa ‘yan sa-kai sun rasa rayukansu ne a kokarin hana garkuwa da ma’auranta, sannan an jikkata wasu daga cikinsu.

Rahotanni na cewa dole ta sanya masu aikin sa-kai janye jiki bayan sun fahimci cewa ‘yan bindigar sun fi karfinsu.

Wani mazaunin unguwar ta Shola da ke cikin Katsina ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun shiga unguwar ne bisa babura jiya dauke da bindigogi suna harbe-harbe.

Mutumin yace ‘yan bindigar sun fasa wani gida ta baya suka shiga. Al’amarin dai yayi sanadin mutuwar mutum biyu sanann mutum biyu suka jikkata.

Ya kuma ce baya ga ma’auratan akwai mutane da dama da aka sace, sai dai bai san adadi ba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da mahara ke aukawa unguwar Shola ba, ko fiye da wata guda ma ‘yan bindiga sun shiga yankin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar wannan hari, inda ya ce jami’ansu sun dukufa don kuɓutar da amarya da angon.

Bugu-da-kari SP Gambo ya ce sun kubutar da wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su a kauyen Tandama cikin karmar hukumar Danja, bayan wani samame da suka kai maboyar ‘yan bidiga.

Haka kuma, ya ce a yankin karamar hukumar Safana ma, sun yi nasarar kashe wani kasurgumin dan fashin daji Albdulkarim Faca-Faca da mutanansa bakwai a karshen mako, bayan barin wutar da wani jirgin yaki ya yi akan maboyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: