‘Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 27, Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutum 9 A Jihar Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim

‘Yan bindiga sun kai wani sabon hari kan manoma a ƙauyukan Jambako, Sakida da Saulawa na Ƙaramar Hukumar Maradun inda suka kashe mutum 25 da garkuwa garkuwa da Mutane da dama a cikin Jihar Zamfara.

Ganau da ido ya ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun kai hari kan mutanen ƙauyen ne a lokacin da suke aiki a gonakinsu da safiyar jiya Asabar.

Wani mazaunin ƙauyen Sakida da ya nemi asakaya sunan sa ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewar, an kashe mutum 21 a Jambako, sannan 7 daga Sakida da Saulawa samu raunuka.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun fara kai wa mutanen Sakidda hari ne a gonakinsu, sai ’yan banga daga Jambako suka garzaya don yaƙar su, inda aka rasa mutum 7 sakamakon musayar wutar da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu.

Kamar yadda nake magana da ku yanzu, mun binne mutum 21 a garin Jambako da rana, yayin da sauran ‘yan ƙauyen Sakida aka binne da yamma kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

A cewar Kakakin Rudunar’ ‘Yan Sanda Jihar Zamfara,ASP Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar wannan harin ya kuma bayyyana cewa, Rundudar ‘Yan Sanda hadin gwuiwar da Jami’an Tsaro sun ceto mutane tara da su ‘yan bindigan su kayi awon gaba da su.

ASP Yazid Abubakar ya kuma tabbatar da cewa, Rundunar ‘Yan Sanda da gamayyar Jami’an Tsaro suna yankunan dan samar da tsaro da kuma zaman lafiya a yanki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: