Yakamata Shugabanin Da Suka Daukar Ma Talakawa Alkawurra Suyi Shirin Cikawa – Blue-Line

Daga Ibrahim Sani Gama

Kungiyar dake fafutukar gagin matasan Najeriya sun samu ayyukan yi da Samar musu da abubuwan dogaro da kai ta kasa, ta shawarci Gwamnatin tarayya da ta jihar kano, da su lalubo hanyoyin sauke nauyin alkawaran da suka dauka a lokacin da suke yakin Neman Zabe.

Shugaban kungiyar na kasa,Alhaji musa Muhammad Alto, Wanda aka fi sani da (Blue Line)ne ya ba da shawarar a yayin da kungiyar tayi taron manema labarai a ofishinsa dake nan kano.

Muhammad Alto yace, makasudun shirya taron shine, kungiyar tayi duba da halin da matasan Arewacin Najeriya suke ciki na rashin ayyukan yi, Wanda rashin ayyukan yi na daya daga cikin abubuwan da suke jefa matasa maza da mata shiga harkar shaye shaye da kwacen waya sauran abubuwa marasa kyau, inda yace, tun yanzu yakamata Gwamnatocin biyu su yi duk maiyiyuwa wajen cika alkawarin da suka yiwa alumma, musamman matasa.

Shugaban yayi kira ga sabon shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da yayi duba akan cire tallafin man fetur da yayi, Wanda hakan zai jefa Alummar kasar nan cikin wahala, musamman wajen hau_hawar farashin kayan masarufi Wanda akasari yana karewane akan Talakawan kasar nan.

Yace, idon kuma, laillai Gwamnatin tarayyar sai ta cire Tallafin man fetur din,To yakamata ta bijiro da wasu hanyoyin magance hauhawar farashin kayayyakin, kasancewar akwai hanyoyi da dama da Gwamnatin take da su wajen magance wannan matsala, tun da Gwamnati uwar kowace.

Muhammad Alto ya kuma, kira ga Gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf da ta bashi dama a matsayinsa na kwararren injiniya domin ba da tashi gudunmawar wajen Samar da ruwan sha a fadin jihar kano da hasken wutar lantarki.

Yace, akwai hanyoyin da masana a kasashen Duniya suke amfani da su wajen magance matsalolin rashin ruwan sha da wutar lantarki,Wanda ya bayyana cewa, kadan daga cikin wasu hanyoyin da ake Samar da su, ta hanyar kafa shigayen bincike, wato(Toitleget)Hayace da take Samar da kudaden shiga Gwamnati da yin amfani da su wajen yiwa alumma kasa ayyukan da kuma, Samar musu da ayyukan yi batare sai sun yi aikin Gwamnati ba.

Shugaban kungiyar yace,wannan kungiya da suka kafa akwai kwararrun matasa da suka yi zurfi wajen kafa kamfanoni na sarrafa kayayyakin cikin gida da ya kamata Gwamnatin jihar kano, ta zauna da su domin ba da ta su gudunmawar da jin irin fasahar Allah ya basu.

Shugaban ya bayyana cewa, ‘Ya’yan kungiyar sun yi tattaki zuwa kasashen ketare domin Neman ilimin Samar da sana,oin dogaro da kai da sanin makamar aiki musamman na kamfanoni da masana,antu da sai saurasu.

A cewarsa,wannan dama ce ga sabuwar wannan Gwamnati da ta yi amfani da wannan dama ta hada hannu da hukumar gudanarwar wannan kungiya wajen magance matsalolin rashin ayyukan yi a fadin jihar kano duba da halin da mayasa suke ciki a yanzu na harkokin shan muggun kwayoyi da kwacen wayoyi Wanda rashin ayyukan yi da rashin ilimin islamiyya Dana Boko suke haifar da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: