Yadda Taron Kungiyar Marubutan Arewancin Nijeriya Na Shekara 2022 Ya Kayatar
Daga Aminu Ahmed Mohd Tsagem
Ranar Juma’ah 9 ga watan Satumba shekarar 2022, rana ce mai dimbin tarihi a garin Katsina yayin da mahalarta taron da gamayyar kungiyoyin marubutan arewacin Nijeriya suka fara shigowa babban birnin jihar Katsina domin halartar taron da gamayyar kungiyoyin suka shirya na wannan shekara mai taken
“Northern Nigeria Indigenous Literatures and languages, Arewa Awards and Annual Congress”.
Taken taron na bana shine INDEGENOUS. LITERATURES AND LANGUAGES’ AS VEHICLE OF TAMING INSECURITY IN NORTHERN NIGERIA.
Masana marubuta manazarta a bangarorin adabi dabam-daban a kasar a sa ran zan yi rudugu akan makalolin da masana za su gabatar a wajen taron.
Ranar Asabar 10 ga watan Satumbar da misalin karfe 10 na safe dakin taron Bello Kofar bai dake sakatariyar gwamnatin jihar Katsina ya fara karbar bakunci manyan baki daga sassa dabam- daban na arewa cin Nijeriya domin ganewa idanuwan su wannan taron.
Manyan bakin da suka halarci taron sun hada da manyan marubuta daga wurare misali- Alh. Aminu Ladan Alan Waka, Wakilin Gwamnan jihar Katsina, kuma kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida, Alh. Abdulkarim Sirika, Alh. Yusuf Dingyadi, Aliyu M Dangida, Danjuma Katsina, Hajia Bilkisu Yusuf Ali, Auwalu Danbarno, Ibrahim Birnin Magaji, Prof. Saleh Abdu, Malamin a jami’ar gwamnati ta Kashere, Jihar Gombe, Prof. Bishir Sallau (Sarkin Askar Yariman Safana), Prof. Idris Isa Funtua Shugaban Kwalejin ilimi ta gwamnati tarayya da ke Katsina.
Sauran sun hada da Engr. Muttaka Rabe Darma, Shugaban Pleasant Library Katsina, Dr Adamu Murtala Mashi, Dan majalisa mai wakiltar Batagarawa da Rimi a majalisar dokokin jihar Katsina, Alh Hamza Rimaye.
Shugaban taron wanda kuma shine shugaban kungiyar marubutan jihar Katsina, Dr Bishir Abu Sabe a farkon taron ya yiwa mahalarta taron barka da zuwa, ya kuma yi fatan cewar bakin za su saki jiki su wala domin sun zo garin kara domin an san Katsina da karamta bakin su
Dr. Abu Sabe ya kuma godewa gwamna Aminu Bello Masari bisa daukar nauyin wannan taro saboda irin gagarumar gudunmuwar da ya bada domin samun nasarar taron.
Shugaban ya kuma godewa Alh. Yazed Abukur da kuma Sardaunan Katsina saboda gudunmuwar da suka bada wajen ganin an samu nasarar gudanar da taron.
Lokacin da yake nasa jawabin, Prof Idris Amali yayi korafi ne akan yadda muka tsinci kawunan mu a arewa na barin kyawawan al’adu da dabi’un tare da rungumar wasu dabi’un turawa wadanda suka shige gaba wajen bata tarbiyar akasarin matasa a arewa, wanda hakan ya sa kauranci da ayyuka daba da kashe-kashen rayukan da daukar mutane akan hanyoyin kasar musammman halin da jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina.
Ya kuma kara bada misalin da wakokin da Dr Mamman Shata yayi mai suna “Allah mai aradu, mai kwarankwatsi” a matsayin wata wakar da shatan yayi a wani da dade lokaci ta zama manuniya ga halin da yankin arewa ya tsinci kansa a ciki na kashe rayuka da dukiya abin ba a cewa komi sai dai addua.
Yayi kira ga gwamnatin Nijeriya ta tashi tsaye a yaki ta’adanci da ‘yan ta’adda tun kafin a karasa sauran abinda ya rage a Arewa.
Bayan jawaban da aka gabatar an karrama wasu fitattun marubuta da sauran manyan mutane da wasu wadanda suka yiwa adabin hausa aiki, manyan marubutan da aka karama sun hada da Aminu Abubakar Alan Waka, Haj. Balaraba Ramat, Arch. Ahmad Musa Dangiwa, Engr Muttaka Rabe Darma, Prof Saidu Muh’d Gusau, Prof Maria Ajiba, Prof. Albishak, Prof Saleh Abdu.
Daga nan kuma aka karrama mai girma Gwamnan jihar Katsina, Alh. Aminu Bello Masari sai kuma shugaban Gidauniyar Hilltop foundation.
An kuma kaddamar da littafin Anologies mai suna Tulu wanda yake dauke da wakokin da guntayen labarai, inda gwamnatin jihar Katsina ta sayi kwafi 3 akan kudi naira miliyan daya, wanda kwamishinan yada labarai bayyana a madadin Gwamna Aminu Bello Masari.
Ranar Lahadi, Mahalarta taron an zagaya da su wuraren tarihi a cikin garin Katsina da Daura, wuraren sun hada da Durbi ta kusheyi domin bakin su ga wuraren tarihi a jihar Katsina.