Yadda mutuwar fitaccen jarumi Yahaya Bankaura ta girgiza masana’antar Kannywood


Daga Abbas A. Dangida

A ranar talata ne Allah ya yiwa ɗaya daga cikin jaruman Kannywood, Umar Yahaya Malunfashi, wanda aka fi sani da Alhaji Yakubu Kafi Gwamna a cikin shirin kwana casa’in mai dogon zango da ake nunawa a gidan talabijin na Arewa 24 rasuwa.

Mahagar Arewa ta ruwaito cewar Yakubu Kafi Gwamna ya rasu ne a yammacin ranar Talata kamar yadda rahotanni suka tabbatar, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Falalu A Ɗorayi daya ne daga cikin jiga-jigai a cikin masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood kuma mai bada umarni ya tabbatar da rasuwar sa a shafukansa na sada zumunta na FACEBOOK Da INSTAGRAM.

Umar Yahaya Malumfashi na daya daga cikin Iyaye Jarumai da suke bada muhimmiyar gudunmawa a masana’antar Kannywood, tun daga diramar dabe (Stage Drama) zuwa ta gidan talabijin da sauransu.

Marigayin wanda ya kasance babban ma’aikaci ne a hukumar hana fasa kwauri ta kasa (Nigerian Customs Service).

Falalu Dorayi a shafukansa na sadarwa, ya yi wa mamacin addu’ar neman Rahamar Allah, Allah Ya bai wa iyaye da iyalai da ƴan uwa hakurin wannan babbab rashi da aka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: