Wata Budurwa Ta Maka Mahaifinta A Kotu
Daga Mujtaba Gali
Wata budurwa mai shekara 20 ta maka mahaifinta a gaban kotu kan kokarin yi mata auren dole.
Matashiyar mai suna Fatima Aliyu daga garin Kaduna ta shaidawa kotun shari’ar musulunci cewa tana da wanda take so amma mahaifinta ke kokarin yi mata auren dole.
Mahaifin ya ce iyayensa kafin rasuwa ne suka zaɓawa diyarsa mijin aure shi ya sa ya ke kokarin cika alkawari.
Alkali Malam Aiyeku Abdulrahman, ya ce duk da cewa mahaifi na da damar zaɓawa ‘yar sa mijin aure, a wannan gabar kokarin tilasta mata bai dace ba.
Ya shawarci mahaifin ya kara hakuri da diyar ta sa.
Alkalin ya bukaci mahaifin ya bai wa ‘yarsa damar gabatar da mutumin da take so sannan a yi bincike, idan babu wani laifi to a bar su su yi aurensu.