Walin Kazaure Ya Ƙaddamar Da Aikin Gyaran Ido Kyauta A Masarautar Ringim

Daga Wakilinmu


Ɗan takarar Sanata mai wakiltar Arewa Maso Yammacin Jigawa a Jam’iyyar APC, Alh. Babangida Hussaini (Walin Kazaure) ya kaddamar da aikin gyaran idanu kyauta, karƙashin Gidauniyarsa mai suna (Walin Kazaure Eye Foundation) a Masarautar Ringim.

A wata sanarwa daga shafin sadarwar zamani na Walin Kazaure Media Crew wadda Comrd Mahmoud Mustapha (LABZY), Shugaban kungiyar Walin Kazaure, Media Team na masarautar Ringim ya wallafa
tace Walin Kazaure ya bayyana cewa wannan shiri na gyaran idanu an bullo da shi ne domin sauƙaƙawa jama’a dake fama da matsalar ciwon idanu a fadin kananan hukumomin 12 da ke arewacin Jigawa maso yamma.

Taron wanda aka gudanar da shi ranar asabar, Walin Kazaure ya kuma bayar da tabbacin cewa za’a cigaba da gudanar da wannan aiki a kowacce shekara domin sauƙakawa jama’a.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da shirin sun nuna jin daɗi matuka tare da yabawa mai girma Walin Kazaure bisa ga wannan yunƙurin kawo cigaban wajen inganta lafiyar al’umma tun kafin ya zama zaɓaɓɓe.

Taron ya samu halartar Dan takarar majalisar tarayya mai wakiltar Ringim da Taura, Hon Sa’ad Wada Taura, tare da shugabannin kananan hukumomin Ringim Da Garki, Shugabannin Jam’iyya da kuma dandazon al’umma magoya bayan jam’iyyar APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: