Walin Kazaure Eye Foundation, Ta Kaddamar Da Gyaran Idanu Kashi Na Biyu Kyauta A Masarautar Ringim

Daga Aliyu Dangida

A kokarinta na cigaba da taimakawa masu karancin gani, Walin Kazaure Eye Foundation ta kaddamar da gyaran idanu kashi na Biyu kyauta a masarautar Ringim.

Alhaji Babangida Hussaini (Walin Kazaure) kuma Ɗan takarar Sanata mai wakiltar shiyyar arewa maso yammacin Jigawa a  karkashin jam’iyyar APC ne ya jagoranci kaddamar da aikin gyaran idanu tare da bayar da magunguna kyauta kashi na biyu.

A jawabin Babangida Hussaini ya bayyana muhimmancin da Ido ke da shi ga rayuwar Ɗan adam, wanda hakan ta sa aka kirkiri wannan Gidauniya domin tallafawa al’umma musamman masu karamin karfi a fadin shiyyar.

Walin Kazaure ya jaddada aniyarsa wajen cigaba da gudanar da wannan aiki a kowace shekara, kamar yadda ya saba tun kafin ya tsunduma harkokin siyasa.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da aikin gyaran idanu, sun bayyana jin daɗi matuƙa, tare da yiwa Walin Kazaure fatan akhairi sakamakon irin wannan ayyuka na alkhairi da suka shafi rayuwar jama’a masu karamin karfi kai tsaye.

Mahangar Arewa ta ruwaito cewar, ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 2022, Walin Kazaure ya kai ziyara asibitin garin Ringim domin kaddamar da aikin gyaran idanun kashi na farko wanda jama’a da dama suka amfana.

Da suke gabatar da nasu jawaban Shugaban karamar hukumar Ringim Hon. Shehu Sule Udi, da Ɗan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Roni, Hon  Usman Hassan Alto, da sauran muhimman suna cikin wadanda suka marawa Babangida Hussaini baya wajen kaddamar da shirin tare da yi masa fatan alkhairi.

An gudanar da Taron ne a babban asibitin garin Ringim ranar asabar 29 ga watan Janairu, na shekarar da muke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: