Tsayar da Gaskiya shine maganin kowane Kalubale ga mai Mulki- Gwani Bade

By Muhammad Sani G. Chinade

Dan takarar kujerar neman shugabancin majalisar karamar hukumar Fune a zaben dake tafe na kananan hukumomin Jihar Yobe a karkashin tutar jam’iyya mai mulkin Jihar ta APC, Honarabul Babagoni Bade, ya bayyana cewar tsayar da gaskiya da rikon amana sune maganin kowane irin kalubale ga kowane mai mulki.

Honarabul Babagoni Bade ya bayyana hakan ne ga wakilin mu yayin tattaunawarsa da shi a garin Damaturu dangane da kudirinsa na takarar shugaban majalisar karamar hukumarsu ta Fune da kuma irin kudirin da ya ke so ya cimma matukar ya samu nasarar darewa mulki a zaben dake tafe a wannan wata na Fabarairu.

Dangane da tambayar da wakilin namu ya yi masa kuwa kan cewar, yanayin yadda karamar hukumar su ta Fune ke da girman gaske cike kuma da kalubale, ko yaya zai iya fuskantar su? ya amsa da cewar, “A duk yayin da mai mulki ko kuma shugaba ya tsayar da gaskiya da kuma rike amanar da Allah SWT ya dora masa na hakkoki babu irin kalubalen da ba zai iya tinkara ba tare kuma da kaiwa ga nasara.”

Dan takarar ya cigaba da cewa, lalle in aka yi duba da irin yanayin karamar hukumarsu ta Fune lalle akwai abubuwa da yawa da ya me yiwuwa magabatan da suka shude sun kauda kai akansu ko kuwa ba su samu sukunin magance su ba musamman kan abin da ya shafi harkokin Ilimi, aikin gona, ruwan sha, da sauran ayyukan raya karkara.

A cewarsa, “Dukkan wadannan abubuwan da na zaiyana da yardar Allah in na shigo mulkin karamar hukumar, da sahalewar Allah SWT zan dukufa wajen ganin na lalubo bakin zaren habaka su”.

Ya ci gaba da cewar, bayan wadancan muhimman ayyukan raya kasa kuma, zan yi iya abin da zan iya wajen ganin na samarwa matasa aikin yi ba wai dukkansu ba amma kuma za a rage musamman ayyukan dogaro da kai tare kuma da nemo daidaikun kungiyoyin cikin gida da NGOs wadanda ke tallafawa jama’a kan harkokin koyar da aikin yi da sauransu.

Don haka ne yake ganin cewarsa, girman karamar hukumar su ta Fune bata ba shi tsoro kasancewar kasa irin Najeriya duk da girmanta mutum guda ne ke mulkar ta, haka Jihar mu ta Yobe duk da girmanta amma mutum daya wadda kuma shine maigidan mu Mai girma Gwamna Mai Mala Buni shike mulkarta ba tare da samun wani tsaiko ba kasancewar ya rike gaskiya da adalci tare da rike amanar jama’ar Jihar bil hakki da gaskiya.

Babagoni Bade ya kuma nemi al’ummarsa ta karamar hukumar Fune da su kada masa kuri’a a ranar zabe don lalubo bakin zaren ciyar da karamar hukumar gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: