Tsakanin gwamnatin Kano da ‘yan Kannywood


Daga Hamisu Lamido Iyantama


DA farko dai a fahimta ta da kuma ɗan ilimin da Allah ya ba ni daidai gwargwado a kan wannan harka ta fim, ban ga laifin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano a kan dakatar da nuna garkuwa da mutane, shaye-shayen ƙwayoyi da ƙwace waya a fim ba. Idan mun duba tare da bibiya, ita kan ta Gwamnatin Tarayya ta kafa hukumomi masu kula da wannan ɓangare ta hanyar inganta sana’ar da masu yin sana’ar. Gwamanti ta yi tanade-tanade masu yawan gaske a kan hakan.

Amma saboda rashin bibiya ko kuma in ce ƙarancin bincike a kan tanadin da waɗannan hukumomi su ka yi mana tun kafin mutum ya fara wannan sana’a su ne dalilan da su ka janyo a duk lokacin da wata hukuma ta bijiro da wata doka domin kawo gyara, ko kuma da ma da akwai wannan doka amma ana son a inganta ta, to daga jin haka sai ka ji an fara ce-ce-ku ce, kowa na faɗin ra’ayin sa, wanda wannan ra’ayi nasa ya saɓa wa dokar, amma fa shi mai yin ƙorafin ya na ganin shi ke da gaskiya alhali ba haka ba ne.

Akwai kundin tsarin yadda Gwamnatin Tarayya ta rubuta hanyoyin da duk wani mai son shirya fim a wannan ƙasa zai bi domin gudanar da harkokin sa. Ya na nan cikin ‘National Film Policy’. Wannan kundi ya hana nuna abubuwa da dama waɗanda su ka jiɓinci fito da tsirarar aikata wasu laifuka manya da ƙanana a fili. Wannan kundi ya haramta nuna abubuwan da ake ta ce-ce-ku-ce a kan su. Amma sakaci na hukumomin da alhakin ya rataya a kan su da son zuciya da rashin zuba ƙwararru su zamo su ne masu kula da waɗannan ɓangarori ya janyo mafiya yawan masu shirya fim su ke ganin abin kamar wani sabo ne. Babu sabunta cikin dokokin da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta yi bisa wannan batu da mu ke ganin ba a kyauta ba.

Ya na da kyau ‘yan’uwa masu wannan sana’a su ƙara faɗaɗa binkice da neman ilimin abin da ba su san shi ba. Kuma su dinga yi wa dokoki da ƙa’idojin sababbi da tsofaffi kallo da idon basira.

Menene laifi don an ce kar mu fito ƙarara mu nuna aiwatar da laifuka a zahiri a halin da ƙasar mu ta tsinci kan ta na rashin tsaro da sauran nau’ika na ta’addanci kala-kala? Ai ya kamata a ce ko cewa aka yi mu dakata da shirin fim a yanzu idan har dakatarwa za ta kawo mana sauƙi cikin al’amura, to mu dakata ɗin.

Idan ni ɗan fim ko mai shirya fim na yarda da cewa mutane na fa’idantuwa idan sun kalli fim ɗin mu, to dole kuma mu yarda cewa idan mu ka saka saɓanin hakan wasu za su iya koyon aikata sharri ko wasu su koyi rashin tarbiyya.

Ba kowa ba ne ya san cewa don ka nuna aikata laifi da masu aikata laifin a cikin fim kafin ka zo ka nuna sakamakon su a ƙarshen fim ba sai nadiran. Ba kowa ba ne ya san cewa kowane fim akwai irin rukunin mutanen da aka shirya wa fim ɗin. Haka ba kowa ba ne ya san cewa hukumomin tace finaifinai su na da ‘classification’ na shekaru ga masu kallon fim.

Da yawan mu sun sani cewa duk wani fim da aka shirya akwai rukunin shekarun mutanen da ake so su kalla kuma an yi fim ɗin ne domin su. Saboda haka, ƙarancin masaniyar haka ta sa masu kallon lamarin ba a dai ɗdai ba su ka fi yawa.

Amma fa a wani ɓangaren dukkan mu mun san cewa shiriya ta Allah ce amma tarbiyyantarwa ta mutum ce. Allah kaɗai ke bada shiriya, shi ya ke shiryar da wanda ya so, ya ɓatar da wanda ya so.

Tun kafin finafinan Hausa su haɓaka babu irin fim ɗin da ba mu gani ba da ‘yan daba, da shaye-shaye iri daban-daban da sace- sace, finafinai irin na ‘Dakuu’, amma mu ba mu koya ba. Allah bai so mu ɓata ba ta dalilin kallon fim.

Idan fim ɗin Hausa na ɓatarwa, to na ƙasashen ƙetare ma na ɓatarwa, duk da cewa fa mun yarda da cewa shiriya ta Allah ce ba wanin sa ba. To ina imanin mu ya ke a nan kenan?

Haƙƙin mu ne mu yi ƙoƙari mu nuna muhimmacin aikata alheri, kuma mu nuna illar aikata sharri.

Tun ran gini tun ran zane! Afakalla ya ɓata rawar sa da tsalle ta hanyar ɓatawa da mutane da dama da su ka fito daga wannan masana’anta. Da yawa mutanen da su ka taimake shi a rayuwa da ‘yan ga-ni-kashe-nin-sa sun ɓata, har da ni kai na! Afakalla ya janyo na yi asarar kuɗaɗe masu yawan gaske, kama daga kwamitin gyaran kasuwa da hukumar ta kafa kuma aka ba ni shugabancin kwamitin da kuɗaɗe na ko kuma in ce kuɗaɗen aljihun mu mu ka aiwatar da wannan kwamiti.

Babu yadda za a ce hukuma ta kafa kwamiti amma ba a ba su kuɗin zama ko zirga-zirga da sadarwa da buga takardu ba. Amma saboda ganin shi namu ne kuma mun yi zaton dukkan mu za mu amfana da ƙudirin da aka ɗora mana nauyi, daga ƙarshe haka mu ka ɓaɓe.

‘Yan’uwa Dangantaka ta Afakallah da sanin ko ni waye a ɓangaren shirin fim ta yi ƙarfin gaske, duk da alaƙa ta da Afakallahu amma ya riƙe mun satifiket, har yanzu bai ba ni ba Fim ɗin da na kashe wa miliyan 1.8 mai suna ‘Wuta A Maƙera’ saboda a cikin fim ɗin wani dattijo ya zagi wani yaro, don yaron ya yi ƙarya dattijon ya ce, “Yanzu wannan shegen yaron cewa ya yi daku ɗan’uwan ta ne?” Sai aka ce sai na cire kalamin “shegen yaron”, ni kuma na ce masa bisa zamantakewa ta Malam Bahaushe iyaye ko manya su na zagin na ƙasa da su cikin fushi. To, har yau shiru ka ke ji tun 2018.

Kuma finafinan nan da na yi, Afakallah ya ƙarfafa mani gwiwa. Da na yi su har faɗa wa mutane ya ke yi cewa shi ya ce na yi. Kuma na ɗebo kuɗi na, su na ajiye a bamki, na zuba, ga su nan jibge gaba na guda biyar, kullum sai zaman makoki na ke yi ita kasuwar ba ta gyaru ba ballantana in kai ko kuɗi na sa dawo.

Afakallah wallahi ya cutar da ni fiye da tunanin ku. Mutum ne da bai san yadda zamantakewa ta ke ba.

Shin ma’aikatan Hukumar Tace Finafinai ta Kano sun fi na Ƙasa ƙwarewa ne da har ‘National’ su ka kalla su ka yaba su ka ba ni satifiket amma na jiha su ka ce ban iya ba? Yaran da tun kafin a haifi wasun su na gama sanin menene dokoki da ƙa’idojin yin fim kuma na yi finafinai ban taɓa kai fim an ce mun ga gyara ba!

Na yi ƙorafi, ya ce min laifin darakta na ne. Abin tambaya a nan shi ne: ni ne na kawo fim Hukumar Tace Finafinai, ba darakta na ba. Yanzu haka za mu dinga rayuwa mu na daƙile juna?

Amma duk da haka ido na ba zai rufe ba, idan maganar gaskiya ta zo zan faɗa ko da ba zan samu goyon baya ba.

Afakallah, ka yi ƙoƙari ka gyara mu’amalar ka da ‘yan ga-ni-kashe-nin ka. Da yawan su su na ganin ka na yi mana dingushe da dungu har da ni a ciki, kuma ka san da haka. Yadda ka ke kiran sunan Allah, haka mu ma mu ke kiran sa inda aka zalunce mu; to ya na nan ya na gani!

Kar ka manta, matattakalar wannan masana’anta ka bi ka tsinci kan ka a inda ka ke, ba don ka fi kowa ba Allah yai maka. Amma a ce kowa sai Allah-wadai?!

Ni dai ban ji daɗin rashin kyakkyawar alaƙar ka da makomar ka ba, wadda ita ce Kannywood. Ko da ka na ganin ka samu duniya ka haye ba za ka dawo cikin mu ba, ka tuna akwai ranar ɗaurin aure, mutuwa ko suna. Ka tuna, akwai ranaar jaje da ranar murna, ai za mu haɗu domin haka.

‘Yan’uwa abokan sana’a, mu sani cewa wannan kujera ta Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta na da hatsarin gaske. Ko wa aka bai wa da wuya a gama lafiya da shi saboda kujera ce da ta ke kare dokokin gwamnati kuma doka ce ta yi wannan hukuma. Afakallah ma’aikacin gwamnati ne, albashi ya ke ɗauka duk wata da sauran su. Saboda haka, alaƙar mu da shi ita ce mu yi abin da bai saɓa mata ba, da daɗi ko ba daɗi. Duk wanda ya bi doka zai zauna lafiya. Mu ci gaba da yin finafinai masu inganci. Kannywood na da ƙwararru da matasa masu hazaƙa. Ku kalli ƙudirin dokar ku yi finafinai bisa dokar, za ku iya kuma sa mutane su kalla su gamsu. Na tabbata da hakan zai yi.

Haka kuma ‘yan’uwa masu sana’a a dinga kallon abubuwa da idon basira. Idan har za ku yi wa Afakallah ihu da surutai a kan wannan ƙudiri, to me hana ku ku yi wa shuganban Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB) wanda shi ne ya fara tabbatar da wannan ƙudiri? Sai dai shi bai hana riƙe makamai ko hana shaye-shaye ba da sauran su ba, ya ce dai lallai ba za su lamunci fifita masu laifi da ba su nasara ba ko kuma kambama masu laifin a cikin fim ba da sauran su. Ina zaton daga wannan jawabi ne da shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa ya yi shi kuma Afakallah ya aro ya kuma zo da nasa tsarin wanda bai yi wa ‘yan Kannywood daɗi ba.

A ilimin aiwatar da fim akwai rashin fahimta idan har aka ce a daina nuna masu laifi ta yadda su ke aikata shi laifin. Idan kuwa hakan ta tabbata, to za kuwa a daina nuna hukuncin da duk wani laifi da aka aikata kuma an daina nuna muhimmancin aikin ɗan sanda ko soja ko alƙali kenan a cikin fim; dole sai an aikata ba daidai ba sannan za a nuna hukuncin wanda ya rataya ga mai laifin a kotu ko wajen jami’an tsaro.

Fim ya na da dokoki da tsarin yadda ake tafiyar da shi. Haka ala’adun mu haka addinin mu. Haka kuma ita hukuma.

Dole ne mai shirya fim ya yi ƙoƙari ya bai wa kowannen su haƙƙin sa ta inda zai gamsar da mai kallo.

Wannan doka da akace Afakalla ya faɗa a kafafen yaɗa labarao, yaushe Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta zauna ta tabbatar da ita Wane ɗan majalisa ne ya gabatar da wannan ƙudiri? Zama nawa aka yi wajen miƙa wannan ƙudiri a majalisa?

Idan kuma majalisa ce ta amince da hakan, mu na buƙatar sabon kwafin dokokin hukumar domin mu karanta. Dole dai sai majalisa ta saka hannu a wannan doka kafin shugabanta ya fito ya fara yaɗawa a duniya.

Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano dai majalisa ce ta zauna ta kafa ta ta yi mata dokoki. Wani mutum shi kaɗai tilo bai isa ya kafa doka ba shi kaɗai, sai dai majalisa. Ko kuma ni ne ban gane ba? Idan ni ne ban gane ba, to ina neman sani a sanar da ni. Ko kuma da ma wannan doka ta na cikin kundin tsarin mulkin hukumar?

Wannan fahimta ta ce, kowa da tasa fahimtar. Kuma ban yi wannan rubutu don in ɓata wa wani ba sai don neman mafita ko gyara. Allah sa mu gane.

Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama babban furodusa ne kuma fitaccen jarumi a Kannywood.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: