Tasiri Da Gudunmawar Sarakunan Kasar Nijar Wajen Bunkasar Al’adu Da Zaman Lafiya

Daga Rabi`u Muhammad Abuhidaya

Wannan rubutu ya samo asali ne daga wani kira da wani dan dan’uwa marubuci Mani Kasumawa Kalgeri, ya yi min game da cewa yakamata na yi dan rubutu game da sarakunan kasarsu ta Nijar game da hibbarsu da kuma adalcinsu ga duk wanda ya kusance su, sakamakon yadda wasu mutane suke ganin cewa Masarautar Agadez ba ta kyauta ba don ta hana ‘yan fim din Hausa(Kannywood) zuwa kasarta da sunan shirin fim, saboda wani Fim da kamfanin 2Effect Empire suka shirya mai suna DAN SARKIN AGADEZ fim din da ya gaza cimma manufar sakon da ake son nunawa jama’a, hasalima fim din tozarci ne ga masarautar da al’adunta.

Babu Shakka masarautun kasar Nijar kaffatanninsu masarautu ne masu cike da haiba da kuma dimbin tarihi kuma masu adalci ga al’ummar da suke shugabanta. Duk mutumin da ya kasance mai bibiyar tarihi zai yarda kuma har ma ya aminta cewa sarakunan kasar Nijar ba su da kyashi ko baiken jin cewa sun taimake ka wajen samar da tarihi da kuma labarin da abin da ya shafe su, kamar yadda na zama ganau ba jiyau ba kamar yadda hausawa ke azancin magana da cewa wai “Gani Ya Kori Ji”.(Tabbas na shaida karamcinsu bisa son addinin da girma a bako)

Zan fara da Masarautar Sultan ta Damagaran a shekarar 2014 na ziyarci fadarsa a wani rangadin bincike da nake yi wanda zai kai ni har gaba da Agadez, Sultan Abubakar Sanda wanda yake mulkin kasar Zinder ya yi matukar farin ciki da zuwa na ya kuma bani masauki tare da bani cikakken lokacin da muka zanta da shi na wani dogon lokaci, har ya gayyace ni zuwa tarbar Ministan cikin gidan kasar wanda zai kawo ziyarar aiki a jihar, amma rashin lokacin da ba ni da shi ban samu damar amsa gayyatar ba, don a daidai lokacin yakamata a ce na isa Agadez akan lokaci, bai damu ba ya yi min wannan uzuri sannan ya bani sakon gaisuwa zuwa ga takwaransa na Agadez wato Sultan Oumar Ibrahim Oumar na Agadez mun yi bankwana da fatan idan na dawo na sake biyawa fada na sanar da shi, hakan kuwa aka yi bayan na dawo na biya masa abin mamaki sha tara arziki aka min a wannan fada cikin barkwanci da raha sosai mu ka yi bankwana da shi da duk mutanen fadar.

Har ila yau daga cikin karamcin wannan sarki shi ne ya dauki nauyi taron kaddamar da kungiyar hadaka ta kasashen Afrika mai suna GIDAUNIYAR ZUMUNCI tare da bikin al’adun hausawa na duniya a jihar Zinder a wannan shekara ta 2018. Haka ma jihar Agadez bayan na isa masarautar na sanar da Sultan zuwa na sai na wuce zuwa masaukina don hutawa saboda gajiyar hanya, bayan kwana daya da zuwa na, ina bacci da rana Sultan ya aiko yana son za mu gana ta hanyar Yariman Agadez Malam Ousseini dan Abbo.

Sultan na Agadez mutum ne mai cike da kwarjini da haiba ga izza wadda za ta nuna maka shi cikakken sarki ne mai daraja ta farko, duk da cewa mu hudu ne a fadar ta shi amma baya magana da ni kai tsaye hasalima bana jin abin da yake fada sai idan ya yi magana a gaya min abin da ya ce, a haka muka tattauna muhimman batutuwa, wani abin burgewa da wannan sarki shi ne son jama’ar kasarsa da kyautata masu, mun yi tafiya da shi zuwa dazuka (idan aka ce daji a kasar Nijar ana nufin wasu garuruwa da suke cikin duwatsu da Sahara ko Kuma kauyukan da suke dan nesa da gari) don halartar taron addu’a na karshen shekara da ake a kasar don neman zaman lafiya da wanzuwar arziki a kasar, motarmu tana gaba ta sultan tana bayanmu sai muka wuce wasu mata da kananan yara a hanya ga dukkan alamu wani garin da ke gaba da su za su je, a cikin motarmu sai sakataren Malaman Jihar Agadez Malam Namadina Alhaji Ousseini ya ce “Zai wahala Sultan bai tsaya yasa a dauko mutanen nan ba”, haka kuwa aka yi ba mu yi nisa ba sai muka ga ana alamta mana cewa mu dakata, bayan mun tsaya muka dawo baya sai muka ga Sultan ya sauko da kansa ya sanya an ba wadannan mutane mota guda wadda ta dauke su tare da kayansu ta kai su garin da za su je, wannan abin ya matukar burgeni na kuma ji na kara kaunar wannan sarki.

A tsawon kwana uku da muka yi a dajin nan wallahi kusan ko yaushe duk abin da aka kaiwa Sultan sai ya sanya an kawo mana da yake masaukanmu suna dab da juna. Bayan an kammala wadannan addu’o’i ba fadarsa ya dawo ba sai da ya wuce zuwa wasu garuruwa don ya gamsu ya kuma tattauna da su, bincikena ya gano cewa wannan sarki kusan koyaushe yana cikin wadannan ayyuka na ziyarar mutanensa da kuma gabatar da ayyukan da suka shafi ci gaban kasarsa duk da cewa akwai sarkin da aka sanya don lura da wadannan garuruwa da ake kira A’ir mai suna Muhammad Suleyman Anastafident, bayan mun dawo sarkin ya sake tambayata akwai wani abu da nake bukata wanda ban samu ba? Na amsa da babu duk wani aiki da ya kai ni na kammala shi har da ma ribar kafa.

A bangaren mutanen Agadez da Nijar kuwa babu wani abu da zan bayyana su da shi sai dai na ce su mutane ne masu son jama’a da kuma girmama baki da kaunar junansa, wani abu da ya sa nake kara yaba musu shi ne yadda suka rike al’adunsu da kuma girmama tarihinsu.

A shekarar 2016 ma na ziyarci fadar sarkin Maradi tare da wani babban dan kasuwa da ke Nijeriya don bude reshen harkar kasuwancinsa garin Maradin, babban abin da ya burge ni shi ne yadda mutanen fadar suka karbe mu da karamci tare nuna jin dadinsu game da wannan abin alheri da zai zo kasarsu, haka ma mahukunta jihar su ma sun nuna jin dadinsu don har wakilin gunduma ya ba mu gayyata ta musamman zuwa gidansa amma da yake muna sauri za mu wuce zuwa Niamey ne, ba mu samu zuwa ba, a wannan bangare ma na yaba musu kwarai.

A saboda haka a matsayina na Marubuci kuma Dan Jarida nake rokon duk wani marubuci ko dan Jarida kai har ma da masu shirya fina-fanai su kasance masu bibiyar tarihi da bincike tare da bibiyar masana kafin yin duk wani aiki wanda zai shiga hannun jama’a saboda gudun irin abin da ya faru a baya game da Fim din Dan Sarkin Agadez, da ma wasu daga cikin rubuce-rubucenmu.

Allah Ya jikan marigayi Gambu mijin Kulum mai wakar barayi mun taba haduwa da shi a jami’ar jihar Kaduna muna zantawa yake nuna min rashin jin dadinsa da abin da wani marubuci yayi masa na rashin adalci, ya ce marubucin ya rubuta karya game da shi da sunan tarihinsa ba tare da kyakkyawan bincike ba.

Bana mantawa lokacin da na ziyarci wata fada a kasar Nijar din dai ta sarki Ahmad Aghali Ibbah sarkin Tanhiya sun sanar da ni tarihinsu tare da cewa duk abin da suka gaya min haka zan rubuta kar na rage kar na kara, kun ga wannan ai shi ne adalci, wani abu da ya sake burgeni da mutanen kasar shi ne lokacin da na je shan ruwa wajensu an samu matsala, amma da na bayyana masu cewa ni bakon sarki ne sai suka kyale ni na tafi abina.(Cikakken rahoton yana cikin labarin ziyararmu birnin Tanhiya) A nan ma ya nuna cewa wannan sarki zaune yake da al’ummarsa lafiya suna kaunarsa yana kaunarsu.

Da fatan wannan tsokaci zai sanya mu amfana wajen yin abin da zai zama karbabbe a kan komai da za mu yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: