Sule Lamido Ya Cika Shekaru 74 Da Haihuwa: Kamfanin Dangida Multi-Media Ltd Ya Taya Shi Murna

Daga Usman D. Aliyu

Shugaban Kamfanin Dangida Multi-Media Ltd, Mawallafan Mujallun Mahangar Arewa, Jigawa A Yau da Hotpen sun taya mai girma tsohon Gwamna jihar Jigawa, Alhaji Dokta Sule Lamido, con murna cikarsa shekaru 74 da haihuwa.

A wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban kamfanin, Aliyu M. Dangida a madadin Daraktoci da sauran ma’aikata ya bayyana Sule Lamido a matsayin jajirtaccen shugaban, kuma jagora abin koyi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimatawa al’umma da kasarsa a tsawon rayuwarsa.

Dangida a cikin takarda yace “Dr. Lamido ya himmatu wajen ciyar da jihar Jigawa inda ta amsa sunanta a lokacin mulkinsa na tsawon shekara 8, ya maida hankalinsa kacokam wajen shimfida ayyukan raya kasa a fadin jihar tare da bunkasa rayuwar al’ummarsa wanda tarihi ba zai manta da wannan gagarumar gudunmawa ta dan kishin kasa abin alfahari ba.

“Ba shakka al’ummar jihar Jigawa da ma Nijeriya shaida ne akan yadda ya maida jihar wani babban birni da ake alfahari da shi a lokacin mulkinsa, ya samu yabo da jinjina da hadin kan al’ummarsa wanda zai yi wahala a manta da ci gaba da ya samar”.

Lamido ya kasance silar dauka darajar jihar Jigawa a idon duniya inda ta tashi daga hedikwatar karamar hukuma zuwa wani babban birni da al’ummar jihar ke alfahari da tunkaho tsabanin shekarun da suka shude.

Kamfanin Dangida ya yiwa Sule Lamido fatan alkhairi da addu’ar Allah Ya kara masa lafiya da jumurin ci gaba da hidimatawa al’umma da kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: