Sule Lamido Ya bani Dama Ne Domin Ci Gaban Jigawa da Matasan Najeriya-Dakta Nuruddeen Muhammad

Aliyu Dangida

Maigirma Tsohon Ministan Harkokin K’asashen Waje Da Kuma Ma’aikatar Yada Labarai Ta Tarayyar Najeriya, Dakta Nuruddeen Muhammad ya ce babban dalilin da ya sa Maigirma Tsohon Gwamnan Jigawa Dakta Sule Lamido (CON) ya zakulo shi daga cikin dubban matasan Jigawa shine domin ci gaban Jihar,  gyara goben matasan Jihar da kuma Najeriya baki daya. 

Tsohon Ministan ya yi wannan kalamai ne a lokacin da  kungiyoyin matasa suka kai masa ziyarar barka da Sallah ranar Talata, 4 ga watan Agusta 2021 a mahaifarsa a cikin garin Hadejiya.

Dakta Nuruddeen ya kara da cewa koma menene su matasan suka gani na tarbiyarsa da cikar kamalarsa har ya ja hankalinsu, toh Dakta Sule Lamido ne ya assasa.

Tsohon Ministan ya kara da cewa hakan kenan na nufin da kai da kaya duk mallakar wuya ne, da ni da ku duk na jagora ne.

Ya yi kira ga matasan da su ci gaba da zage dantse domin ganin cewa gobensu ta fi yau a bisa doron tarbiyya da jagoranci irin na maigirman tsohon Gwamnan, Jagoran PDP na Jigawa da kuma talakawan Najeriya gaba daya

Tunda farko dai masu magana da yawun kungiyoyin a bayanansu daban-daban sun ce dalilin wannan ziyara ta su shi ne domin yin alfahari da shi a matsayinsa na ‘Da Halak, Malak ga Jagoran talakawan Najeriya, Dakta Sule Lamido da kuma jaddada goyon bayansu ga Maigirma Ministan da kuma kara masa karfin gwiwa a bisa duk wani kudurce- kudurcensa na ci gaban Al’umma, musamman irin tsare-tsaren da Gidauniyar Unik Impact ta ke fitarwa a duk fadin Jihar Jigawa da kuma  kokari da tashar ridiyo ta Sawaba FM da ya gina a cikin garin Hadejiya ta ke bayarwa ta hanyoyi daban-daban don ci gaban Al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: