Sojojin Najeriya Sun Kai Farmaki Sansanonin Boko Haram, Sun Kashe ‘Yan Ta’addar Ma Su Yawan A Sambisa

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Rundunar sojin Najeriya ta Operation Hadin Kai ta bayyana cewa ta kashe mayakan Boko Haram masu yawan gaske da har zuwa yanzu ba a tantance adadinsu ba, yayin da ta kai farmaki kan sansanonin ‘yan ta’adda 6 a yankin dajin Sambisa da ke kusa da yankin Bama cikin jihar Borno.

A wani rahoto da aka tattara na nuna cewa an kashe ‘yan ta’addan ne bayan wani kutsawa cikin yankunansu da sojoji na 21 Task Force Brigade Bama suka yi tare da hadin gwiwar rundunar farar hula ta (CJTF), suka yi a yankunansu a ranar 25 ga Maris, 2023.

Wata majiyar leken asiri ta shaidawa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da ta’addanci a tafkin Chadi cewa sojojin sun yi nasarar kashe ‘yan ta’addan a yankunan Bula Agaida, Bula Yaga, Bula Lambai, Kuluri, Bula Umar da New Churchur a karamar hukumar Bama.

Majiyar ta ce a yayin farmakin sojojin sun gano tare da lalata wani katafaren sansanin ‘yan Boko Haram da ke tsakanin Bula Agaida da Bula Yaga. Sojojin sun kuma gano tare da lalata kasuwar ‘yan ta’addar.

Zagazola ya fahimci cewa, a lokacin da ake sintiri na yaki domin tsarkake yankunan da sojojin suka yi arangama da wasu ‘yan ta’adda, sun kuma kashe su tare da gano wata motar kirar Toyota Hilux.

Majiyar ta tabbatar da cewa galibin ‘yan ta’addan sun bar sansanoninsu yayin da sojojin suka lalata wadanda aka sake kafawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: