Shugaban NECAS Ya Kaddamar Da Kwamitin Kwato Lamunin Da Kungiyar Ta Baiwa Manoma A Shekarun 2018/2019 A Yobe

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

A ci gaba da bin umarnin shugaban kungiyar ta NECAS na kasa shugaban kungiyar reshen jihar Yobe Hon Nuhu Baba Hassan ya kafa wani kwamitin gwiwa da ya kunshi jami’an ‘yan sanda na farin kaya DSS, ‘yan sanda da Jami’an tsaron farar hula (NSCDC) sarakunan gargajiya don gudanar da wani gagarumin yunkuri na dawo da lamunin CBN-ABP. rancen da aka bayar a cikin shekarun 2018 & 2019.

A cewar Hon Nuhu Baba Hassan Shugaban Hukumar NECAS ta Jihar Yobe, ya kamata a biya kudin da tsabar kudi ko da kayayyaki kamar yadda aka bayyana tun farko a cikin yarjejeniyar lamuni da aka yi tsakanin kungiyar da wasu manoman Jihar.

Don haka ana sanar da manoman da suka ci gajiyar wannan shirin don biyan bukatun kansu da su gaggauta amsawa tare da biyan bashin da ake bin su gaba daya, don gujewa fuskantar fushin hukuma kasancewar karkashin kungiyar ta NECAS ne aka bada wannan rance.

“A cewar sa matukar Wanda ya karbi wannan rance ya gaza zuwa don biya to kuwa labudda ya zama wajibi a tuntubi mutumin da ya yi lamuni gare shi, don dawo da duk wasu kudade da kayayyakin da aka ba shi, kamar yadda aka amince da su a cikin fom ɗin da aka cike mai dauke da sharudda kafin bada rance.”

Wannan umarni ya zo ne sakamakon umarnin da mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da cewa dole ne ku dawo da duka, ba wani bangare na rancen ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: