Shugaban Jam’iyyar APC Jihar Yobe Ya Halarci Sallar Jana’izar Marigayi Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Fika
Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Yobe Alhaji Muhammad Gadaka ya halarci sallar jana’izar Alh Adamu Usman Bazam Madakin Gudi, tsohon zababben shugaban karamar hukumar Fika.
A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun sakatariyar kula da manema labarai ta shugaban Hajiya Sa’adatu Maina ta bayyanawa jaridar mahanga Arewa cewa, babban limamin masarauta Ibrahim Mohammad ne ya jagoranci sallar jana’izar a fadar Mai Martaba Mai Gudi da ke garin Gadaka a karamar hukumar Fika da misalin karfe 2:05 na rana.
Muhammad Gadaka, wanda ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa mamacin ‘yan uwa kuma Allah ya ba su damar jure wanna babban rashin da ba za a iya misalta shi ba. Ya kuma yi addu’ar Allah ya sanya shi a Aljannatul Firdausi.
Marigayin ya rasu yana da shekaru 69 a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Yobe Damaturu bayan ya sha fama da rashin lafiya. Ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya goma sha tara (19).
Marigayi Adamu Bazam wanda aka taba zabar a matsayin shugaban karamar hukumar Fika mutum ne mai tsananin kirki, mai saukin kai, kuma kai tsaye wanda ko da yaushe yana gauraya da kowane nau’in mutanen da ke kewaye da shi.
Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin gwamna Alh idi Barde Gubana da sakataren gwamnatin jiha Alh Baba Mallam wali da kwamishinan ma’aikatar yada labarai da al’adu Mohammad Lamin da na al’amuran jin kai da kula da iftila’i Dr Abubakar Garba iliya.
Sauran sun hada da wasu ‘yan majalisar Jiha da suka hada da Hon Suleman Yakubu, Hon ishaku Daya, da kuma Hon. Saminu Musa Lawan.
Sai kuma masu ba da shawara na musamman, kan Muhalli, gidaje da lafiya, da shugabannin kananan hukumomi, Janar Manajan na hukumar dab’i ta Jiha da sauran shugabannin hukumomin gwamnati da na ‘yan agaji da kuma daruruwan masu jajantawa daga kowane bangare na jihar da makwabciyar jihar Gombe da sauransu.