Sheikh Aminu Daurawa ya roki Mahajjatan da su sa Nijeriya cikin add`uo`insu

Mu`azu Hardawa Daga Makka

An shawarci Alhazai da suka isa kasar Saudi Arabiya domin sauke farralin aikin Hajjin bana daga Nijeriya su sanya kasa cikin add`uah don ganin an kawo karshen matsalolin da ke faruwa na rashin tsaro da sauransu.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa daga jihar Kano na cikin Malaman da suka kasance masu wayar da kan mahajjata a karkashin hukumar jin dadin Alhazai ta Nijeriya NAHCON, Wakilinmu a kasar Saudiya ya tattauna da shi a birnin Makka don jin ta bakinsa game da sharruda da yadda ake gudanar da ibadar aikin Hajji.

Aikin Hajji ya kasance daya daga cikin shikashikan musulunci guda biyar wacce idan aka yi aikin yadda aka yi umarni sakamako shine gidan Aljannah.

Inda Sheikh Daurawa ya roki ‘yan Nijeriya a duk inda suke a kasa mai tsarki da Nijeriya da kuma.kasashen duniya da su kasance masu kishi da yiwa kasar add`uah don samun ingancin zaman lafiya.

Inda ya ce abin takaici ne lamarin da ke faruwa na rashin tsaro a Nijeriya don haka ya kamata kowa ya bayar da gudummawa don yin add`uar ganin Allah ya kawo karshen.matsalar.

Sheikh Aminu Daurawa ya roki Alhazan bana da su sanya kasar cikin add`uah. ta musamman.  Bayan haka ya roki alhazan su kasance masu bin doka da oda a lokacin zaman su a kasar Saudiyya tare da yin aiki da ilmin da aka ba su na gudanar da aikin

Hajji kamar yadda shari`a ta tanadar don yin Hajji karbabbiya wacce ba ta da sakamako sai gidan aljannah. Don haka ya yi fatan Alhazai za su fita filin Arfa da Minna da Muzdalifa lafiya su gama aiki lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: