SERAP Ta Kai Gwamnatin Najeriya Ƙara Kotun ECOWAS

Daga BBC Hausa

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a Najeriya ta kai ƙarar gwamnatin ƙasar gaban kotun ECOWAS saboda kasa binciken batun bututan da ake zargin satar mai da su tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022.

ƙungiyar na so gwamnatin ƙasar ta binciko tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu kan batun a gaban kotu.

Hakan na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan aka gano bututu 58 da ake amfani da su wajen satar man, bayan da aka ja su zuwa tsakiyar teku, inda ake loda man a manyan jiragen ruwa domin sayar da shi.

Najeriya dai ta dogara ne kacokan kan ɗanyen mai da take haƙowa kuma kuɗaɗen shigarta na cikin matsala saboda satar man, kamar yadda jami’ai ke faɗa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: