Saudiyya Ta Buge Argentina A Gasar Wasa
Daga BBC Hausa
Saudiyya ta doke Argentina 2-1 a wasan farko na rukunin C na gasar cin kofin duniya da ake ci gaba da yi a Qatar.
Lionel Messi ne ya fara ci wa Argentina a bugun fenareti minti 10 da fara wasa.
To amma a minti na 48, wato jim kadan bayan dawowa hutun rabin lokaci ne Saudiyya ta farke ta hannun Al-Shehri.
Kuma minti biyar bayan haka a minti na 53 Al-Dawsari ya ci wa Saudiyya kwallo ta biyu.
A yanzu Saudiyya ce ke jan teburin da maki uku, yayin da Argentina take ta karshe.
Idan anjima za a buga wasa na biyu a rukunin tsakanin Poland da Mexico.