Saudiyya Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 10 Ga ‘Yan Gudun Hijirar Ukraine

Daga BBC Hausa

Gwamnatin Saudiyya ta bayar da taimakon magani da makwanci da ya kai na dala miliyan10 domin ga ‘yan gudun hijirar Ukraine sama da miliyan daya.

Shugaban hukumar bayar da agaji a duniya ta kasar Saudiyya wato King Salman Humanitarian Aid and Relief Center (KSrelief), Dr. Abdullah Al Rabeeah shi ne ya sanar da haka a Poland.

Ya jaddada kudurin kasar tasa na taimaka wa ‘yan gudun hijirar da suka tsere daga Ukraine zuwa Poland da sauran kasashe makwabta da cewa hakan na daga kudurin kasar na taimaka wa mutanen da ke cikin mawuyacin hali a fadin duniya.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a hedikwatar ofishin jakadancin Saudiyyar da ke babban birnin Poland din Warsaw, jiya Litinin.

Hukumar bayar da agajin ta Saudiyya tana gudanar da ayyukan jin-kai da suka zarta 2,000 a kasashe 85 a fadin duniya.

Ayyukan da suka hada da samar da abinci da kula da lafiya da bayar da ilimi da samar da ruwa da tsaftar muhalli da sauransu, in ji shugaban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: