Sakataren Gwamnatin Katsina ya yi kira ga ma`aurata da su rinka gwajin cutar sikila kafin aure
Daga Aliyu Dangida
An yi kira ga al’umma da su dinga ziyartar cibiyoyin lafiya domin yi gwajin kafin su daura aure domin kaucewa da kamuwa da cutar sikila.
Sakataran gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Muntari Lawal ne ya bada shawarar a ofishin sa dake a gidan gwamnati yayin da yake karbar bakunci wata tawaga daga kungiyar masu fama da larurar a Jihar Katsina a karkashin jagorancin shugabar kungiyar Laila Muhammad.
Alh. Muntari Lawal yace “Cutar sikila cuta ce, wadda ta ke da sarkarkiya domin kuwa galibin masu fama da ita, ada ba su san cewa ita ce ba. Saboda haka ya zama wajibi ga al’umma da su bi ka’idojin litika don yin gwaji don kaucewa da kamuwa tare da kara yada ta a cikin al’umma”.
Daga karshe ya godewa shugabar kungiyar tare da `yan tawagar ta akan ziyarar da suka kawo masa. Ya Kuma ba su tabbacin cewa “zai yi bakin kokarinsa domin ganin an taimakawa wannan kungiya”. In ji Muntari Lawal.
Da take mai da jawabi, shugabar kungiyar Laila Muhammad ta ce sun zo ne, domin ziyarar ban girma da kuma kawo kokon barar su na neman taimako akan yadda gwamnatin za ta kawo masu wani tsari don samun sauki wajen sayen magungunan su.
Ta kara da cewar gwamnatin ta shiga domin kara taimaka masu, wajen ganin ana bin dokin gwaji kafin aure domin kara dakile tare da kaucewa kamuwar ciwo.
Laila Muhammad daga karshe ta gode wa sakataren gwamnatin yadda aka tarbe su.
Rahoto daga Mobile Media Crew (Katsina)