Sabon Kwamandan NSCDC Ya Dauki Alwashi Magance Manyan Laifufuka A Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim

A yanzu haka da ‘yan bindiga suka cigaban da kashe-kashen mutane da garkuwa da su, sabon kwamandan rundunar farin kaya (NSCDC) Sani Mustafa ya dauki alwashin magance matsalar tsaro da manyan laifufuka da suka addabi Jihar Zamfara.

Kwamanda Sani Mustafa ya bayyyana haka ne a lokacin da ya ke amsar ragamar kama aiki daga hannun takwaran sa mai barin gado, Muhammad Bello Muazu a Hedikwatar Hukumar da ke Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

A nasa jawabin, Kwamanda Sani Mustafa ya yi alkawarin bayar da duk gudunmawar sa wajen yaki da matsalar tsaro da masu aikata laifuka a jihar.

Don haka kwamanda Sani Mustafa ya umarci dukkanin jami’an rundunar da ke jihar Zamfara da su guji cin mutuncin jama’a, su guji cin zarafin jama’a amma su kasance masu tsayin daka da da’a wajen gudanar da ayyukansu.

Babban abin da ya fi daukar hankali shi ne gabatar da tutar hidimar rundunar da Kwamanda Muhammad Bello Mu’azu a mai barin gado zuwa ga kwamandan mai jiran gado, Kwamanda Sani Mustafa.

Kwamnadan mai barin gado ya bayyana nasarorin da ya samu zuwansa Jihar ta Zamfara, ta kokarinsa na magance matsalar tsaro da manyan laifufuka da kuma cigaba jami’an rundunar na karin girma ga ma’aikatan dadai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: