Rundunar Sojojin Najeriya Ta Gargadi Masu Kokarin Tayar Da Zaune Tsaye A Zaben 2023

Daga Mujtaba Gali

Babban hafsan sojojin Najeriya Laftana Janar Faruk Yahaya ya gargadi masu neman tayar da zaune tsaye cewa rundunar sojojin kasar za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar ba su yi tsarin dimukradiyyar kasar illa ba.

Janar Yahaya ya kuma ce rundunar za ta dauki tsauraran matakai kan kungiyoyin da ke shirin yamutsa babban zaben da ke tafe a fadin kasar.

Babban hafsan na jawabi ne a ranar Litinin yayin wani taron kara wa juna sani na kwana uku da rundunar ta shirya wa sojojinta a cibiyar horar da sojoji ta TRADOC da ke Minna babban Jihar Neja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: