Rundunar Ƴan sandan Najeriya Ta Haramta Amfani Da SPY Plate Number


Daga Muhammad Aminu Kabir

A wata sanarwa da Magana da yawun Rundunar Ƴan sandan CSP OLUMUYIWA ADEJOBI ya sanyawa hannu mai taken “Tsaron cikin gida Sufeto Janaral Usman Alkali Baba ya haramta amfani da Lambar da take ɗauke da sunan SPY a faɗin ƙasar nan baki ɗaya.

Sanarwar ta ƙara da cewa Sufeton Ƴan sandan ya bada Umarnin ƙwace duk wata lamba da take ɗauke da sunan SPY babu wane ko wanene aka ganshi da ita daga yanzu za’a ƙwace ta, kuma an soke lasisin amfani da Lambar har illa ma Shaa Allah.

Wannan dokar an sanya ta dole ne saboda masu amfani da wannan Lambar suna amfani da ita wajen karya dokokin tuƙi da sauran dokokin ƙasa da dama suna ɓoyewa akan wannan damar da suka samu wajen keta doka.

Sufeto Janaral ya Umarci duk wani Jami’in Ɗan Sanda da yake aiki da manyan Jami’in Gwamnati ya tabbatar da anyi amfani da wannan dokar kazalika sauran Jami’an tsaro su ma su tabbatar da an bi wannan dokar, yace duk wanda bai bi wannan dokar ba Hukuma za ta chafke shi.

Haka nan kuma sanarwar ta ƙara da cewa ƙwamishinonin Ƴan sanda 36 na faɗin ƙasar nan da kuma Abuja kazalika Mataimakan Sufeto Janaral da suke kula da shiyyoyin ƙasar nan su tabbatar da an bi wannan dokar an kuma ƙwace duk wata lamba ta SPY da yanzu ake amfani da ita.

Ya ƙara da cewa Jami’an tsaro kar su kama kowa wanda yake amfani da wannan Lambar in ba Jami’in Ɗan Sanda bane, ma’ana wanda yaƙi bin dokar za’a ƙwace Lambar ne kawai a bar shi ya kama gaban shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: