Ronaldo Ya Kai Al-Nassr Wasan Ƙarshe A Gasar Zakarun Larabawa


Daga Mujtaba Gali


Kaftin ɗin Al Nassr, Cristiano Ronaldo ya kai wasan ƙarshe karon farko tun bayan komawarsa taka leda a Saudiyya.


Ronaldo ya jagoranci Al Nassr a wasan da ta doke takwararta ta ƙasar Iraqi, Al-Shorta da ci 1-0, a wasan dab da na ƙarshe na gasar cin kofin Zakarun kasashen Larabawa, a birnin Abha na kudancin ƙasar.


Ɗan wasan na Portugal ya ci ƙwallo a bugun fenareti a minti na 75 da fara wasan, a lokacin da ɗan wasan bayan Al-Shorta, Faisal Jasim Nafil Al-Manaa ya yi wa Sadio Mane ƙeta.


Ronaldo ya ci wa Al-Nassr ƙwallo huɗu a wasanni huɗu a gasar cin kofin sarki Salman ta zakarun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar kasashen Larabawa.


Tun daga zagayen farko na gasar, Ronaldo ne ya fi kowanne ɗan wasa cin ƙwallo har kawo yanzu.


Al Nassr za ta kara da Al-Hilal a wasan ƙarshe na gasar da za a buga ranar Asabar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: