Rarara Ya Shirya Taron Addu’a Ga Kasa da Rabawa Yan Kannywood Kudi a Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Shahararren mawakin siyasar nan na Hausa, kuma shugaban kungiyar  mawaka ta 13+13, Alhaji  Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara), ya shirya taron  addu’a na musamman a kan rashin tsaro da ke addabar Arewaci da ma wasu sassa na Nijeriya, da kuma yi wadanda suka rasu yan wannan masana’atar ta  Kannywood addu’a.

An shirya taron addu’ar ne a babban dakin taro  da ke kan tatin murtala Muhammad way Jihar Kano, a Ranar  Litinin da ta gabata, da zummar Allah ya kawo ƙarshen rashin tsaro a ƙasar.

Da ya ke jawabi a yayin taron addu’ar, Rarara ya ce ya zama wajibi a haɗu a yi wa ƙasa addu’a a bisa mawuyacin halin da ta tsinci kanta.

A cewar sa, rashin tsaron da ya addabi Arewa da ma wasu sassa a ƙasar nan, na matukar bukatar addu’a, musamman ma yadda babban zaɓe na 2023 ke tunkaro wa.

Ya ƙara da cewa Musulmai da Kiristoci ya kamata su duƙufa da addu’a a masallatai da coci-coci domin neman ɗauki daga Ubangiji.

Rarara ya kuma ce taron bashi da wata alaƙa da siyasa, “illa dai a nemo mafita a wajen Ubangiji domin samun zaman lafiya.

“Idan babu zaman lafiya, ko mu ma ba za mu iya yin harkar fim ɗin mu ba. Saboda haka muna kira ga ƴan Nijeriya, Musulmai da Kiristoci, da mu dage da addu’a a masallatai, coci-coci da kuma gida-gida domin Allah Ya bamu zaman lafiya,”a cewar  Rarara.

Ya kuma ƙara da cewa taron ya yi amfani wajen kara danƙon zumunci tsakanin ƴan masana’antar Kannywood.

Darakta a masana’atar Kannywood kuma daya daga cikin Yan kwamitin  Ali Gumzak ya ce wannan taro da Dauda Rarara ya shirya gagarumin aiki ne na tarihi da wani ma bai  taba tunanin yin sa ba.

“Ka ga dai bayan an tashi  taron ya bi kowa da Gudunmawar kudi ga danyen nama da aka raba, wannan abin ayaba masa ne kwarai da gaske”.

Da ya ke na sa bayanin, Shugaban hukumar shirya Finafinai ta kasa reshen jihar Kano wato Malam Ado Ahmad Gidandabino MON ya ce babu shakka wannan abu ne mai kyau a shirya taro na addua domin samun zaman lafiya a kasa da jiha da kuma  yi wa matattu na Kannywood addu’a.

“Lallai ya hada zumumci  mutane da aka dade baa hadu ba, wasu a Jos wasu Kaduna da  sauransu jihohin kasar nan duk mun hadu mun gaisa kuma  munyi musanyar lambar waya wannan abu ne mai kyau”.

Sannan ya yi kira da masu da dama da ke cikin wannan masana’ata da su yi koyi da Dauda Rarara wajen amfani da damar da suke da ita wajen kyautatawa mutane da tunawa da wadanda suka rigamu gidan gaskiya.

Babban Jarumi a masana’atar da ya yi tattaki daga Jos ya ba ya ce ” A gaskiya wannan bawan Allah ya cancanci mu yaba masa kuma mu jinjina masa kuma mu yi farinciki da abinda muka ga an gabatar na karatun alkurani mai girma da addu’oi” ta bakin Al’amin Buhuri.

Da take tofa albarkacin bakinta Hadiza Muhammad da aka Sani da Hadizan Saima ta ce ” a gaskiya munji Dadi mu yi farinciki da da shirya wannan taro domin da ana shirya irin wannan taron adduaa da wasu masifu da ke damun masana’atar da ba su dame mu ba, domin duk abinda ya gagara aka koma ga Allah to Allah zai jibinci lamarin don haka muna godiya da wannan abu”. inji Hadizan Saima

Taron dai ya samu halartar sama da alarammomi 200 da suka  yi karatun alkurani a cikin su har da shi kan sa Dauda Rarara, inda suka yi sauka goma sha tara.

Kazalika taro  ya samu halartar tsofaffin da sababbin yan Kannywood na jahohin Nigeriya.

Bayan kammala saukar karatun Alƙur’anin ne, to  kuma sai aka shiga yin addu’o’i.

Sannan aka yanka raƙuma guda biyu domin yin sadaka, daga nan ne.

aka raba kuɗi ga dukkan waɗanɗa su ka halarci taron, wanda shi kansa Rarara ya raba da hannunsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: