Ranar Maleriya Ta Duniya: Yadda Sauyin-Yanayi Da Rigakafi Suke Shafar Yaki Da Zazzabin Cizon Sauro


Daga Mujtaba Gali

Ranar 25 ga watan Afrilu ce Ranar Cutar Zazzabin Cizon Sauro ta Duniya lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke fadakarwa game da hadin guiwa wajen yaki da samun duniyar da babu sauran cutar maleriya.

A yayin da ruwan rigakafin cutar maleriya na farko ke taimakawa a yakin da ake yi da kwayar cutar, sauyin yanayi na nufin cewa tana iya yaduwa a sabbin yankuna.

Ana samun kamuwa da cutar ta maleriya sama da miliyan 240 a ko wace shekara, inda cutar ke hallaka mutane fiye da 400,000 a fadin kasashe daban-daban.

Amma a yayin da aka kaddamar da shirin bayar da ruwan allurar rigakafin na farko da hukumar lafiya ta duniya WHO ta amince da shi ya taimaka wa yakin da ake yi da cutar, sauyin yanayi da dumamar duniya na nufin cewa za ta iya yaduwa a sabbin yankunan da ba a taba samu a baya ba.

Yaduwa mai hatsari
“Dumamar yanayi yana kara wa sauro karfin yada kwayar cutar maleriya da ke haddasa cutar zazzabin,” in ji Dakta Isabel Fletcher, manajar sashen fasahar tattara bayanan kimiyya ta kungiyar bayar da agaji ta Wellcome Trust.

Ta yi gargadin cewa: “Sauyin yanayi zai sa karin wasu yankuna na duniya samun sauraye masu yada cutar.

A yayin da duniya ke kara dumama, ana fatagar cutar maleriya za ta kara bazuwa zuwa sabbin yankunan kan tudu yadda kwayar cutar za ta iya yaduwa.

Kamar yadda kwamitin gwamnatoci kan sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya (IPCC) ya bayyana, koda an aiwatar da duka manufofin rage yawan fitar da iskar carbon da gwamnatoci suka bullo da su nan da shekarar 2020, duniya za ta cigaba da dumama zuwa ma’aunin zafi 3.2C a cikin wannan karnin.

Burin kasashen duniya shi ne, a rage dumamar yanayi zuwa kasa da ma’anin zafi 1.5C ta hanyar rage yawan fitar da gurbatacciyar iskar carbon.

Baya ga karuwar dumamar yanayi, masu bincike sun yi gargadin cewa saukar ruwan sama da kuma damshi har ma da yanayin fari ka iya haddasa karuwar saurayen da ke yada kwayar cutar maleriya cikin sauri a inda ba a taba bayar da rahoton cutar a baya ba.

“Bincike ya yi nuni cewa kasashen yankin Caribbean da kuma a kasar Brazil cewa a duk lokacin abkuwar fari, mutane kan ajiye karin ruwa. Hakan na haifar da wuraren zama ga sauraye.

Shi ya sa lokacin fari, za a iya samun karuwar yada cutar zazzabin dengue,” Dakta Fletcher ta ce.

Akwai fargabar cewa muddin hakan ta faru ga zazzabin dengue, zai faru ga zazzabin maleriya shi ma.

Sauyin yanayi ka kuma iya rage yaduwar zutar zazzabin maleriya a wasu yankunan da suka fi kyau, hakan ya sa Dakta Fletcher ke tunanin cewa samun gagarumar fahimtar tasirin sauyin yanayin dumama zai zama muhimmi a cigaba da yaki da cutar.

“Ta hanyar kirkirar hasashe kan fuskantar barazana a nan gaba, za mu iya gano yawan al’ummar da ke cikin fuskantar hadari don haka za a dauki matakai yadda ya kamata,” ta ce.

Mene ne alamomin kamuwa da cutar maleriya?
Maleriya cuta ce mai tsanani wacce sauraye ke yadawa, da kuma kan haddasa mutuwa idan ba a gano tare da yin magani da gaggawa ba. Alamomin sun kunshi:
• zazzabi mai zafi, zufa da jin sanyi
• ciwon kai da dimuwa
• gajiya da jin barci (musamman a kananan yara)
• jin rashin lafiya, ciwon ciki, da gudawa
• rashin ci abinci
• ciwon jiki
• fata ta koma launin rawaya ko kodewar idanu
• bushewar makogwaro, tari da matsalar numfashi

Hukumar ta kididdige cewa ruwan rigakaafin zai iya ceton rayukan karin kananan yaran Afirka 40,000 zuwa 80,000 a ko wace shekara.

“Mun duba tasirin ruwan rigakafin bayan shekaru biyu kuma yanayin sahihancinsa.

Abinda muka gano shi ne cewa ruwan rigakafin na ba shi da matsala kuma ana iya jure masa,” in ji Dakta Mary Hamel, da ke jagorantar aiwatar da shirin WHO na yin rigakafin.

“Lokacin wadannan shekaru biyu na karbar rigakafin, an samu gagarumar nasara na raguwar kwanciyar asibiti kan tsananin cutar ta maleriya da kashi daya bisa uku.”

Katafaren kamfanin sarrafa magunguna na BioNTech shima ya kirkiro wani ruwan rigakafin cutar maleriya ta hanyar amfani da hanyar fasahar zamani ta mRNA da aka yi amfani da ita a karon farko a ruwan rigakafinta na cutar korona.

Ta yaya ruwan rigakafin ke aiki? Ana samu a wadace?

Maleriya kwayar cuta ce da ke kutsawa tare da lalata kwayoyin halittar jinin dan adama don yaduwa ta hanyar sauraye masu zukar jinni.

Na’ukan ruwan rigakafi na RTS, S na maganin akasarin kwayoyin cuta mafi hadari a Afirka: Plasmodium falciparum.


A lokacin da sauro ya ciji mutum, wannan kwayar cuta kan shiga cikin hanyoyin jinin kawyoyin halittar hanta.

An hada ruwan rigakafin don hada kwayar cutar daga kama hanta, inda ta kan kara girma da kuma yadu ta sake shiga cikin hanyoyin jinin tare da kama kwayoyin halittar jinni, inda daga nan suke nuna alamomin kamuwa da cutar.

Ruwan rigakafin na bukatar a yi wa mutum sau uku kafin ya yi aiki sosai, ana bayar da guda ukun farko wata guda a tsakani, daga watanni biyar, da shida da kuma bakwai, kana a karshen watanni 18.

Kwararru a fannin kiwon lafiya sun bayar da shawarar amfani da allurar rigakafin hade da tsare-tsare da dama na kariya daga kamuwa da cututtuka da kuma rage yaduwar cututtuka da farkon fari.

WHO na sa ran za bukatar ruwan rigakafin zai zarce miliyan 80 a ko wace shekara, musamman a yankin kudu da Saharar Afirka.

Wannan bukata mai yawa za ta zo da na ta kalubalen.


“Samar da shi zai zarta bukatarsa a yayin da kamfanonin sarrafawar ke kara yawan yadda yake samar da ruwan rigakafin,” in ji Dakta Hamel.

Yanzu haka kamfani daya ne kawai mai sarrafawa, GlaxoSmithKline (GSK).

“Shirin shi ne na kamfanin GSK ya a kara yawan ruwan rigakafin zuwa guda miliyan 15 a ko wace shekara,”

Dakta Hamel ya ce.
“Ya zama dole mu hada kawunanmu da wajen tabbatar da cewa an samu wadatattun ruwan rigakafi da zai kai ga kananan yaran da ke fuskantar barazanar kamuwa da matsanaciyar cutar zazzabin cizon sauro na maleriya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: