Ramadan: Mataimakin Kakakin Majalisar Borno Ya Raba Wa Marayu Tufafi

Daga Sani Gazas Chinade, Maiduguri

A ranar Alhamis ne mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Borno, BOSHA, Rt Hon Abdullahi Askira, ya kaddamar da rabon kayan sawa ga yara kimanin 218 wadanda akasarinsu marayu ne da rikicin Boko Haram a karamar hukumar Askira/Uba ya rutsa da iyayen su da ya ki su ga samun kan su a matsayin Marayu.

Wannan karimcin wanda shi ne taron shekara-shekara don baiwa marasa galihu, musamman yara marayu sanya sabbin kayayyaki lokacin bukukuwa, musamman ma bikin Eid-el-Fitr Sallah wanda aka shirya gudanarwa tsakanin Lahadi da Litinin mai zuwa.

Mataimakin kakakin majalisar Hon. Askira ya yabawa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum bisa sanya hannu kan dokar kare hakkin yara bayan da shugabannin kungiyar majalisar dokokin Jihar BOSHA suka gabatar masa a farkon wannan shekarar.

Dan majalisar ya ce baya ga baiwa marasa galihu fifiko, yana taimakawa mazabarsa ta hanyar kawo musu wasu ayyuka da suka shafi jama’a kamar gina lungu da sako na ajujuwa da cibiyoyin kula da lafiya da samar da kayan amfanin gona da kayayyakin rage radadin talauci ga al’ummar mazabar. .

Da yake kaddamar da rabon kayan sawa da sauran kyautuka na Sallah ga marayu a Askira/Uba, dan majalisar ya ce ya dauki nauyin marayu da dama don ci gaba da karatunsu a cibiyoyin ilimi daban-daban, don haka ya yi kira ga masu hannu da shuni da su ma su sa hannun su don taimaka wa masu rauni a cikin al’umma.

“A koyaushe ina nuna matukar jin daɗi lokacin da nake ɗaukar nauyin ɗalibai, musamman marayu don yin karatu a makarantu daban-daban, rarraba musu riguna / tufafi kyauta da littattafan darussa daban-daban, takalma, jakunkuna na makaranta da sauran abubuwa,” in ji shi.

Dan majalisar ya tabbatar wa al’ummar mazabar sa kan kudirinsa na dorewar wannan mataki, ya kuma yi kira gare su da su yi addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.

“Ku ’ya’yana ne, kuma duk abin da ya same ku yana faruwa da ni kuma. Ina so in tabbatar muku da cewa a halin da kuke ciki muna tare,” ya shaida wa marayun.

A halin da ake ciki, mataimakin kakakin majalisar ya taya yaran jihar Borno murna tare da godewa Gwamna Zulum, wanda tun daga lokacin da ya sanya hannu kan dokar kare hakkin yara ta jihar Borno.

Ya ce wannan ci gaban wata nasara ce ga yaran Borno, ciki har da amincewa da tsarin doka na kare su daga daukar aikin tilas da amfani da kungiyoyi masu dauke da makamai, bautar da yara da cin zarafinsu da sauran laifukan cin zarafinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: