PSG Ta Dauki Lucas Hernandez Daga Bayern Munich


Daga BBC

Paris St-Germain ta sayi dan wasan baya Lucas Hernandez mai shekaru 27 daga Bayern Munich kan kuɗi fan miliyan 34.

Dan wasan, wanda ya lashe gasar cin kofin duniya a 2018 tare da tawagar Faransa, ya lashe kofuna uku da Bayern a kakar wasa ta 2019-20 – kakarsa ta farko a kungiyar.

Bayan da Hernandez ya lashe gasar lig da kofin guda biyu, ya taimaka wa kungiyar da Hansi Flick ke jagoranta, wajen doke PSG inda ta lashe gasar zakarun Turai.

Hernandez, wanda ya buga wa zakarun Bundesliga wasa sau 107, ya kuma zura kwallo biyu a raga, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru biyar.

Ya taka muhimmiyar rawa a gasar cin kofin duniya da Faransa ta lashe a Rasha a 2018, amma duk da cewa an zaɓe shi a tawagar Faransa a gasar cin kofin duniya a Qatar 2022, raunin gwiwa da ya samu a wasansu da Australia ya hana shi buga sauran wasannin gasar.

Sun kai wasan ƙarshe na gasar karo na biyu a jere, amma Argentina ta doke su a bugun fenariti.

Kanensa, Theo Hernandez, yana taka leda a gasar a Seria A tare da kungiyar AC Milan .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: