PRP : Dan Takarar Gwamnan Kano Dawisu ya Kai Ziyara Bebeji

Daga Ibrahim Hamisu

Dan takarar jamiyyar PRP na jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai ya kai ziyara  garin Gargai dake karamar hukumar Bebeje a jiya Asabar.

Bebeji wanda mahaifa ce ta dan takarar mataimakin Gwamnan Jam’iyar PRP a Kano, wato Mallam Shazali Muhammad Gargai.

Ta cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, Salihu Tanko ya bayyana cewa manufar  ziyarar shi ne kai gaisawa ga mahaifiyar Hon. Gargai, da sauran manyan gari ciki harda Dagacin garin Gargai, da sauran manyan gari.

Kazalika,  tawagar ta  karasa garin Kuki shi ma da ke kusa da Bebeji domin gaishe da mai girma hakimin Kuki da Dagacin garin.

Tawagar dai ta samu halartar dan takarar majalisar taraiya na Rano, Kibiya, Bunkure na PRP, da dan takarar majalisar jiha mai wakiltar Bebeji a PRP, da shugabannin jam’iyar PRP na kananen hukumomi da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: