Ni ne Bahaushe na farko a Katsina da ya fara sana’ar hoto.. Abashe Kofar Guga

*Na je Makka sau 30 da sana’ar daukar hoto

A garin Katsina, da wasu jihohi makwafta sunan Alhaji Abashe Mai Hoto, ba ɓoyayya bane, musamman ga masu sauraren wakokin Dakta Mamman Shata Katsina,

Alhaji Abashe mai Hoto, shine Mutum na farko Bahaushe a ƙasar Katsina da ya fara sana’ar Daukar Hoto, Inda ya kwashe Shekaru Hamsin da biyar a akan sana’ar tun a shekarar 1966, zuwa yanzu, kamar yanda Jaridun Katsina City News, ta zanta dashi:

“Ni sunana Abashe, an haifeni Unguwar Kofar Guga a garin Katsina, tun tasowata dai na fara karatun addini, a nan Unguwar tamu, daga nan aka kaini Zariya wajen karatu, a zamanin Sarki Jafaru, bayan nayi karatu, ina nan, kuma daga Zariya akwai wani yaya na da muke taɓa Kasuwanci, a tare, amma ba na zama waje guda ba, muna yawo garuruwa, Irin su Kagoro, Naija, Jos, da Kogi, da yake ban yi, karatun zamani ba, sai yace ya kamata in dogara da kai na, wace sana’a nafi so…? sai ya sa a koya mani. Sai nace ma shi, sana’ar daukar hoto, sai yace wannan sana’ar ba ta Hausawa ba ce, in dai canza wata, to ni dai da yake abinda nafi so, ke nan sai na fahimtar da shi, kuma nace masa, zan taimaki Al’umma ta wannan sana’ar ko ba komai ba Hausawa ke yin ta ba, kuma yanzu zamani ya zo komi sai da hoto, ko Makka za ka sai an yi maka hoto.

Sai ya aminta da haka, ya dauke ni ya kai ni a Jos, aka kai ni Makaranta koyon Aikin Hoto. To aƙa’idar karatun shekara biyu ne, amma da yake ina son karatun, sai na maida hankali, cikin Ikon Allah a wata tara, na kammala kuma aka bani sakamako (Certificate) na dawo, Yayana ya sai mun kyamarori, da kayan aiki, sosai na shigo Katsina da su, na fara aikin hoto, a lokacin nan Katsina mutum biyu ne Inyamurai ke sana`ar hoto, kuma su ma sun ji tsoro sun bar garin saboda ba’a dade da yin rikicin Biyafara ba, sai ya zamana a ‘yan kasuwa, ba na gwamnati ba, ni ne Bahaushe na farko a Katsina da ya fara sana’ar hoto.

Lallai mun ga nasara da ci gaba sosai, a rayuwa a cikin wannan sana’ar, tsawon shekaru hamsin da biyar, na je Makka sau talatin, tsawon shekarun nan ban taba babbar sallah a gida ba, har ta kai ga ina sha’awar in ga na yi babbar sallah a gida Nijeriya.

Ban dakata da zuwa Makka ba sai a lokacin da Mangal ya samar da jirgi mallakarsa (Max air), shi ma mahaifiyar Mangal din ta ƙi yarda, saboda tace, babu wanda take so yayi mata hoto a Makka sai ni, haka dai mu kayi ta gungurawa cikin nasara. Ni dai tunda na fara wannan sana’ar ban taba ganin ci baya ba, zuwa na Makka na farko, a lokacin Sa’idu Barda yana shugaban hukumar Alhazai ta ƙasa a shekarar 1977, ya bani kujera bayan da na yi mashi hotunan bikin diyar shi.

Alaƙata da shata, shi ma hoto, ya haɗa mu, wata rana shata……..

Katsina City News

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: