Najeriya Za Ta Haɗa Gwiwa da Google don Daƙile Tasoshin da ke yi Mata Ƙafar Ungulu a Youtube

Daga BBC Hausa

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta haɗa gwiwa da kamfanin intanet na Google wajen daƙile wasu tasoshin yaɗa hotunan bidiyo a dandalin Youtube da suke ƙoƙarin yi wa gwamnati ƙafar ungulu.

Ministan yaɗa labaran ƙasar ne ya bayyana aniyar gwamnatin a wata ganawar da ya yi da masu kamfanin Google.

Ministan yada labaran Najeriya, Alhaji Lai Mohammed ne ya sanar da aniyar gwamnatin Najeriyar, a wata ganawar da ya yi da wani ayarin kamfanin na Google a Abuja a jiya.

Ya ce irin wadannan tasoshi ba su da wani aiki sai yaɗa labaran ƙarya da cusa gaba a tsakanin al’ummar ƙasar.

Cikin wata sanarwa, Alhaji Lai Mohammed ya ce zai so kamfanin Google ya duba hanyoyin da zai yi maganin wasu tasoshi da na wasu kungiyoyin da gwamnati ta haramta wanzuwarsu ta hanyar toshe su da adireshinsu na sada bayanai ko saƙonni da sauran hanyoyin da suke bi suna yada manufofinsu ta intanet.

Ministan ya yi misali da ƙungiyar IPOB, mai fafutukar kafa ƙasar Biafra, wadda ya ce haramtacciya ce, kuma shafin google shi ne danadalin da mafi yawan mabiyanta ke bibiya, kuma ta nan take yaɗa aniyarta ta haddasa husuma da wargaza ƙasa.

A cewar Ministan, Najeriya na cikin kasashen duniya, waɗanda mutanensu ke gaba-gaba wajen amfani da kafafen sada zumunta na zamani irin su Google da Facebook da Tik-tok da Twitter da kuma Whatsapp, wadanda adadinsu ya kai fiye da miliyan dari.

Alhaji Lai Mohammed ya ce irin waɗannan kafofin suna taimakawa sosai, saboda suna bai wa ƴan Najeriya damar hulɗa da juna da musayen ra’ayi, har ma da gudanar da harkokin kasuwanci da na siyasa.

Amma kamar yadda ya koka, wasu ɓata-gari na amfani da su wajen yi gwamnati zagon-ƙasa.

Jagoran ayarin kamfanin na Google, Mr Charles Murito ya ce kamfanin ya fito da wani shiri na horar da ƴan kasa a kan yadda za su dinga nazarin abubuwan da ake wallafawa ko yadawa ta intanet.

Hakan zai sa su fahinci abubuwan da ke da illa don ankarar da kamfanin, yana cewa shi kamfanin nasu ba ya goyon bayan masu yaɗa abubuwan da za su haddasa tashin hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: