Najeriya na Kokarin Bunkasa Kasuwancin Kwakwa

Daga BBC Hausa

Yawancin yankunan Najeriya suna da kyakkyawan yanayin da za a iya shukawa da samar da kwakwa.

Amma duk da haka kasar na siyo kashi 70 cikin dari na wannan dan itace mai muhimmancin gaske da ake sarrafawa a yi abubuwa daban-daban, kama daga abin ci da abin sha da kuma man girki da na shafe-shafe.

Ganin yadda bukatar kwakwa ke karuwa a cikin Najeriya da kuma kasashen duniya, yanzu akwai shirye-shirye na sa kasar ta zama mai dogaro da kai a fannin samar da kwakwar.A unguwar Isolo da ke tsakiyar babbar cibiyar kasuwanci ta Najeriya, wato Lagos, Toyin Kappo-Kolawole tana gudanar da wata ‘yar karamar masana’anta ta sarrafa kwakwa.

Tana yin  madara da ruwa da garin fulawa da kuma kayan kwalan da makulashe, duk da kwakwar.

Ta fara gudanar da wannan kasuwancin nata ne inda ta sanya wa masana’antar suna De-Cribbs Cocogry Coconut, a 2018.

Tana samo kwakwar daga garin Badagry, na gabar teku a jihar ta Lagos, inda nan ne aka fi samar da kwakawar a Najeriya.

Bayan da sana’ar tata ta bunkasa sai ya kasance ba ta samun wadatacciyar kwakwar a Najeriya, abin da ya sa ta rika sayo ta daga Ghana.

“Wannan ya sa kaya na tsada, hakan na nufin ina samun raguwar masu ciniki,’’ in ji ta.

Ana sarrafa wannan dan itace ta hanyoyi da dama, a yi abubuwa iri-iri, kama daga  abinci da kayan sha da man shafawa da gawayi da kasa da makamashi da dai sauransu.

Bukatar kayayyakin da ake yi daga kwakwa a kasashen duniya ta karu sosai tun daga shekarun 2000.

A dalilin wannan an samu karuwar mutanen da ke shiga wannan harka ta samarwa da sarrafa kwakwa domin cin wannan gajiya.

Hatta lokacin da abubuwa suka yi tsada jama’a na bukatar kayayyakin da ake yi da kwakwar – kasuwarsu ba ta raguwa.

A watan da ya gabata Najeriya ta kaddamar da shirin dasa itatuwan kwakwar a Badagry a wani mataki na bunkasa harkar.

Wannan na daga cikin kudurin kungiyar masu nomawa da sarrafa da kuma sayar da kwakwar a Najeriya, (Nacoppman) domin sa kasar ta zama mai dogaro da kai.A bara Najeriya ta sayi tan dubu 500 na kwakwa daga waje, domin sarrafawa ta samar da mai da kayan abinci da na sha, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna.

Na ziyarci wata gona da ke da nisan tafiyar sa’a biyu daga Abuja, a mota, wadda wasu ma’aurata – Ray Davies da mijinta, wani Manjo Janar mai ritaya (John Davies) suke gudanarwa.

Ma’auratan sun kafa gonar ne shekara shida da ta gabata, inda yawanci suke samar da ‘ya’yan itace da suka hada da lemo da ayaba da kuma fasa-dabur (soursop).

Sai kuma a shekara ta 2021, suka hada da kwakwa a irin ‘ya’yan itacen da suke samarwa a katafariyar gonar tasu mai girman hekta 20.

Sakamakon rashin wadatar kwakwar da kuma samuwar karin masu sarrafa ta a Najeriya, abin da ya sa kasar dole take siyo kwakwar daga kasashe irin su Togo da Ghana da Kwadebuwa (Ivory Coast), manoma irin su Davies na fatan cike wannan gibi.

Shugabar kungiyar manoma da masu sarrafawa da sayar da kwakwar a Najeriya (Nacoppman), Nma Okoroji, ta ce mutane na kara samun wayewa da fahimtar cewa harka ce ta samun kudi.

Ta ce, kwakwa za ta iya kara yawan kudin da Najeriya ke samu.

”Muna da kyakkyawan yanayi da filin nomanta da kuma manoman, da su yi ta.

Kamata ya yi a ce muna ma fitar da ita kasashe maimakon mu sayo daga wasu kasashen,” in ji ta.

Ms Okoroji na aiki karkashin wani shiri na bunkasa samar da kwakwar a Najeriya tare da tallafin gwamnati (mai suna Cosin).

Shirin da a karkashinsa ake kudurin dasa itatuwan kwakwa a fili mai girman hekta 10,000 a yawancin jihohin Najeriya 36 zuwa shekara ta 2027.

Sai dai babbar matsalar ita ce ta samun ingantaccen irin kwakwar.

Iri mafi inganci shi ne na aure wanda aka samar daga, hadin doguwar bishiyar kwakwar ta Afirka ta Yamma da kuma gajeruwa ta yankin Asia.

Ta auren tana fara ‘ya’ya a cikin shekara hudu zuwa biyar, ba kamar gajeruwa ta Asia ba, wadda take fara ‘ya’ya a cikin shekara biyu da rabi zuwa uku.

To amma kuma ita ta aure kwararru sun samar da ita ne musamman domin noma na kasuwanci – samun ‘ya’yan kwakwar da yawa kuma masu girma.

Abiodun Oyelekan, wanda ke da gonar kwakwar a Badagry, ya ce yana da kyau a yi amfani da kwakwar ‘yar aure saboda yawan ‘ya’yan da take samarwa a shekara.

Sai dai ya ce, tana da tsada domin duk dashe daya ya kai kusan dala 6 (sama da naira dubu 3,600), wanda hakan ya sa ta fi karfin yawancin kananan manoma.

Ma’aikatar sarrafa kwakwa na bukatar wutar lantarki

Aikin hukumar bunkasa noman kwakwa ta Lagos (Lascoda), shi ne ta taimaka wajen bunkasa harkar ta yadda za a rika samar da ita sosai ga kasuwa.

Shugaban hukumar Dapo Olakulehin ya ce jihar ita ce kan gaba wajen samar da kwakwa a Najeriya.

”To amma ba a iya wadata kasar da ita saboda karuwar yawan masu sarrafa ta a cikin shekara 10 zuwa 15 da ta gabata,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “A shekara uku da ta gabata, lokacin da muka ga alamar karuwar bukatarta sai muka rika karfafa wa mutane guiwa kan su shiga harkar domin samar da ita yadda ake bukata.

A shekara hudu zuwa biyar masu zuwa za a fara ganin tasirin hakan idan bishiyoyin suka fara ‘ya’ya.”

Hukumar bunkasa noman kwakwar ta Lagos tana da fili inda take samar da dashen itaciyar da take raba wa jama’a.

A bara ta raba wa manoma har dashe dubu 200 kyauta, amma duk da haka ba su isa ba.

A bana kuwa dashe dubu 80 kawai hukumar ta iya rabawa, wanda wannan na nufin masu sarrafa kwakwar a Najeriya dole ne su ci gaba da sayo ta daga waje zuwa wani lokaci.

Wani babban jami’i a Ma’aikatar Masana’antu da kasuwanci da Zuba Jari ta Najeriyar, Kaura Arimiye, ya ce gwamnati ta dauki wannan harka a matsayin wata hanya ta rage yawan marassa aikin yi da kuma rage dogaron da kasar ke yi a kan man fetur domin samun kudi daga waje.

Ebun Feludu – Wata mai kamfanin sarrafa kwakwar, wajen yin abubuwa daban-daban (mai suna JAM), tana ganin idan gwamnati na son cimma bukatar hakan to sai ta bunkasa muhimman abubuwan inganta rayuwa kamar wutar lantarki da tituna da sauransu.

Ms Feludu ta ce Najeriya ta yi kaurin suna wajen rashin wutar lantarki, haka ma tituna ba su da kyau.

Sannan kuma ta ce akwai bukatar gwamnatin ta rage dawainiya da kudin fitar da kayan zuwa kasuwannin duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: