Najeriya : Jami’an Shige Da Fice Sun Kama ‘Yan Ci-Rani 33

Daga BBC Hausa

Jami’an hukumar shige da fice ta Najeriya reshen jihar Ogun ta kama ‘yan ci-ranin Chadi da Togo 33 a wasu yankunan jihar biyu.

Rahotonni sun ambato babban kwantirola mai lura da jihar Yakubu Jibrin na cewa waɗanda ake zargin ba su da takardar izinin shiga Najeriya sannan ba sa ɗauke da ko wacce irin shaida.

Ya kuma alkawarce cewa za a mayar da mutanen ƙasashensu bayan an yi tuntuɓa tsakanin ƙasashen nasu na asali da kuma gwamnatin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: