Nadin Da Shugaba Tinubu Ya Yiwa Barista Nyeson Wike Abin A Yaba Ne – Hon Khalid Bello

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Kungiyar makiyaya ta Kulen Allah Cattle Rearers Association of Nigeria (KACRAN) ta yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa bajintar da ya yi na nadin Barista Nyeson Wike, tsohon gwamnan jihar River a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja wadda yin hakan abin a yaba ne.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Honarabul Khalid Muhammad Bello shugaban KACRAN na kasa a tattaunawsa da wakilinmu a garin Damaturu, ya ce, tafiyar siyasar Barrister Wike, tun ma kafin muhimmiyar rawar da ya taka a zaben 2023 hakan ya sa ya samu nasarar wajen tantance shi a yayin tantance ministoci a majalisar dokokin kasar wadda kan hakan bai fuskanci wata turjiya ba musamman ganin irin juriyarsa da kwazonsa.

“Yunkurin da ya yi na tabbatar da tsarin babban birnin tarayya Abuja ya kara jaddada aniyarsa ta tabbatar da ingancin ofishinsa.’Mu a KACRAN’ mun yi imanin cewa, matakin da Shugaba Tinubu ya dauka na nada Barista Wike, dan Kudu na farko da ya rike wannan mukami, wani muhimmin mataki ne na samar da hadin kai da fahimtar juna tsakanin ’yan Najeriya.”

Nadin na Barista Wike na nuni da wani sabon salo na karfafa alaka da ‘yan uwantaka a tsakanin al’ummomin tarayyar Najeriya.

“Ba za mu yi watsi da irin nasarorin da Barista Wike ya samu ba, ciki har da aiwatar da wani shiri na musamman na bunkasa kiwo a Jihar sa ta Ribas, wanda ke nuna iya rike mukaminsa da kuma bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban kasa.”

“Muna amfani da wannan damar don tunatar da Barrister Wike babban alhakin da ke tattare da sabon aikinsa a matsayinsa na Ministan babban birnin tarayya Abuja, ana sa ran ya yi wa dukkan ‘yan kasa adalci tare da gujewa duk wani tsari ko ayyuka na daukar fansa da ka iya cin zarafin abokan hamayyar siyasa.

“Muna roƙonsa ya ci gaba da nuna juriya dangane da duk wani zargi mai ma’ana da zai iya fuskanta, kuma ya dauki hakan in ta taso a matsayn gyara kayan ka maimakon akasin hakan.”

Kamata ya yi cikin wannan lokaci nasa ya kasance da gaskiya, rikon amana, da kyautatawa ga daukacin ‘yan Nijeriya.

“Muna ba wa Barista Wike shawara mai karfi da ya yi amfani da matsayinsa wajen bunkasa Abuja, tare mayar da ita a matsayin wata cibiya ta hada kan ‘yan kasa ba tare da nuna wani bambancin ta kowace fuska ba kuwa.”

Kuma.Samun damarsa ga jama’a zai tabbatar da cewa an ji kuma an aiwatar da kyawawan ra’ayoyi da hangen nesa don ci gaban birnin da mazaunansa.

“Muna kuma kira gare shi da ya tuna cewa matsayinsa na Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja yana daya daga cikin manyan mukamai a Najeriya, idan aka yi la’akari da shi na mazaunin ‘yan Najeriya daban-daban da ke birnin.”

Wannan dama wacce yawanci ke zuwa sau daya, yakamata ya yi amfani da ita cikin adalci da gaskiya, domin a bar gadon ci gaba da hadin kai.

“A karshe muna kira ga masu ruwa da tsaki da su marawa Barista Nyesom Wike baya a kan manufarsa don isar da mafi kyawun manufar wannan gwamnati don amfanar al’ummar Najeriya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: