Mutum 36 Sun Rasa Rayukansu a Bukuyyum
Daga BBC Hausa
Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawallan Muradun ya ce mutum 36 aka kashe a karamar hukumar Bukkuyum.
Cikin wata tattaunawa da BBC Matawalle ya ce sakamakon harin da aka kai a kananan hukumomin Anka da Bubukkuyum ya ziyarar gani da ido don tabbatar da irin ɓarnar da ƴan bindigar suka yi.
Ya ce yanzu haka suna da sunaye da bayanan mutanen da aka kashe ɗin.
Gwamnan ya ce daga Bukkuyum Anka zai wuce domin ya tabbatar da abin da rahotanni ke ambatowa cewa sama da mutum 200 aka kashe.
Ya ce zai yi iya kokarinsa domin ganin cewa an mayar da duka wadanda suka gudu daga wadannan kauyuka zuwa garuruwansu nan da mako guda.