Mutum 134 Sun Mutu Tare Da Asarar Dukiya Mai Yawa A Jigawa

Daga BBC Hausa

Gwamnatin jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce akalla mutum 134 ne suka mutu, yayin da aka yi hasarar dukiya ta kusan naira tiriliyan 1.5, sakamakon ambaliya ruwa da jihar ke fuskanta.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito mataimakin gwamnan jihar Alhaji Umar Namadi, na bayyana hakan ranar Asabar, lokacin da ya karbi bakuncin shugaban Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF mai kula da jihohin Kano, da Katsina, da jigawa Rahman Rihub Mahmud Fara,

Ya kara da cewa ruwan na ci gaba da yin yankin gabashin jihar, inda ya ce kananan hukumomin Birninwa, da Kirikasamma na cikin hatsari.

Mataimakin Gwamnan ya ce ambaliyar ta shafi kusan mutum 272,189, inda gidaje kusan 76,887 suka rushe.

Ya ci gaba da cewa akwai karamar hukuma guda da ambaliyar ya shafe hanyar da ke hada ta da jihar.

Daga karshe ya yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran kungiyoyin agaji da su taimaka wa jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: