Muna Son Shugaban da zai Kula da Bukatar Matune ne- Shugaban Kungiyar Matasan.

Tattaunawa

Ganin yarda ake cigaba da Fuskantar matsalar tsaro a Sassa daban – daban a kasar nan, Kuma zaben shekara ta 2023 ke kara saho kai.


Haka Kuma ana ta samun kiraye- kirayen cewar mulkin kasar nan a shakara ta 2023 daya koma Kudanci, daga Kungiyoyi daban – daban na Matasa daga Arewaci dama Kudancin Kasa, tare Kuma da ambatar Sunayen wasu da su fito don yin Takarar Shugabancin wannan kasa.

Wan nan yasa na tatauna da Shugaban gamayyar Kungiyoyin Matasan arewacin Najeriya wato Nastura Ashir Sharif, wanda har’ila yau shine Kuma Shugaban Matasa na Kungiyar Tuntuba ta Arewa wato( ACF) a takaice, don sanin ko ya suke kallon makomar kasar tare Kuma da sanin kowaye dan takarar su a zabe mai zuwa na 2023 dama sauran batutuwa a Tattaunawarsa na Jaridar Mahangar Arewa.

Ga dai yarda Tattaunawarsa ta guda na da wakilin mu a Kaduna ABDULLAHI ALHASSAN.

Mahangar Arewa: koya kuke kallon makomar kasar nan……..?

Nastura Ashir Sharif. Wato Al’muran suna da dimautuwa, wato dimauta dan Adam duk tunaninsa da Kuma fargaba acikin yarda ake kallon makomar kasar sakamakon abubuwa Kamar guda biyar.


Na farko matsalar ta rashin tsoro datake cigaba.

Na biyu rushewar tattalin arzikin kasa na.


Na Uku talauci da kullum yake dada karuwa.


Mutane suna rasa Jarikansu sakamakon tsadar rayuwa aksar, akwai magana ta hauhawar farashi na kayan amfanin na kasa, sannan ga Shugabanci mara nagarta mara Kyau.

To duk inda aka samu wayan nan abubuwa hakika dole duk wani dan kasa hankalinsa ya tashi domin yasan makamar kasar tana cikin hatsari, ga rashin aiyukanyi na Matasa ko kayi makaranta ko bakayi ba.

To wadannan duka wato Alkalima ne suke nuna cewar kwantacceyar fitina a cikin kasa, indai akwai wayan nan abubuwa to sai dai fatammu ubangiji Allah ya kawo wa kasan mafita.


Kuma ya ubangiji Allah ya kawo Mata Shugaban na nagari, domin ldan ansamu Shugaban ni nagari wadan da zasu lya rike amanar kasa, su tabbatar wadanda suke Ma’aikata dana kasa dasu basuyi amfani da wata dama ba suna satar kudaden kasa ba.
Zuwa inda akasa abin ya je musu to in ansamu Shugaban ni wanda zasu tasaya kan wannen abubuwa to insha Allahu kasar nan zata samu makoma tagari, Kuma muna fatan samun hakan. Shugabannin da zasu jajirce kan gyaran wan Al’muran.

Mahangar Arewa:To ko waye dan takarar ku a zabe mai zuwa2023 ..?

Nastura Ashir Sharif: To mu a kungiyance bamu da dan takara, amma dan takarar mu shine Shugaba wanda yake Adali mai gaskiya, wanda yake zai lya rike Mutanen kasar nan ya yaki wadannan munannan aiyuka da suke faruwa acikin kasar nan shine mukeso.

Kuma duk Shugaban da zai lya Jagoranci nagari ya zauna ya rike Mutanen tsakani da Allah, babu kabilanci, babu Almundahana, ba yaudara, babu karya, to mu ko a lna yake maraba dashi, in dai zai zauna ya yi tsakanin sa da Allah ya taimaki Mutane ya kawo karshen rashin tsaro nan.


Atursassa a toshe duk hanyoyi da Ma’aikata da wasu yan Siyasa suke hada kai suke kwashe kudaden kasa suna barin Mutanen kasa cikin rigima ta talauci da tashin hankali.
to mu ko waye wan nan shine dan takarar mu.

Kuma bawai Shugaban kasa kawai muke magana ba, muna magana kan ko wane ofis da za’a zabe Mutane su tsaya su zabe Mutane na kwarai, ba Mutane dasu zo su baka magi, ko gishiri, ko omo, ko awara, ko wani dan Kudin da ba zai lsheka cefanen rana guda ba ,aje a basu kuri’a ba, ba irin wayan nan Mutanen ba.

Mu tunanin mu a samu Mutane Sahihai kuma nagartattu, Kuma lafiyayyu, ba irin Mutanen da shekaru suka janye mu su ba.
Masu shiga halin dimuwa suna neman Mutumin da zai taimaka musu har zuwa karshen rayuwarsu, ace Kuma a dauko su a dora musu nauyi dawainiyar al’umma ba, mu bama goyon bayan irin wan nan Mutane masu irin wan nan shekaru.

Muna so a samo Mutane ingantattu lafiyayyu wanda kwakwalwarsu take tafiya tana yin aikin da ya kamata.


Kuma jikinsu zai lya daukar dawainiyar sa hankalinsu ba wanda kurin zai dauki mulki ya bar yara kanana suje suna sha’aninsu, ko Kuma wasu Mutane da suke kusa dashi, ko yan barandarsa, saboda shi ya riga ya tsufa takansa kawai yake yi.


A nemi Shugabanni to ko lna aka duba suna da gogewa da cencenta da lafiya da lokaci da zasu lya bayarwa a gyara kasa da gina kasa mu shine dan takarar mu.


Ba kawai Shugaban kasa muna so harda Sauran mukamai Kamar, Sanatoci, yan Majalisar Tarayya da na Jihohi, da ma sauran duk muka man wan dan Yan shine irin Mutanen da muka so a Shugabanci.

Mahangar Arewa:Ganin cewar ana ta kiraye- kirayen daga Kungiyoyin Matasa Kasar nan kudunci dama Arewaci na cewar wasu fito don tsayawa takara?

Nastura Ashir Sharif:To ai kasan lokacine na zabe saboda haka da dillalan Mutane dana Siyasa duk fitowa suke suna baje kolin su, Kuma akwai Mutanen da komai lalacewar Mutum haka zasu yi mai talla babu abinda ya dame su ,ln dai zaka basu kudi baruwansu da lalacewar sa , bukatar al’umma su, su dai kansu kawai suka sani.

Sobada haka Mutane su gane cewar fa yanzu bada bane da za’a chanja musu gurbatattatun Mutane saboda bukatar wasu, su bude ldanuwansu su zabi Mutane Jajirtatatu wandan da zasu kula da bukata tunsu, da Kuma damuwar su.

Amma masu kiraye – kiraye baka lya hana su ba amma laile Mutane su tsaya su zabe Mutane kirki Masu Mutunci da zasu kula da damuwar su ba kawai ko wani dan takara ba wan nan shine Matsayar mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: