Muna Da Yakinin Sabon Gwamnan Zai Dora Daga Inda Kwankwaso Ya Tsaya A Lokacin Sa Na Aikin Raya Jihar Kano – AG Muftahu

Daga Rabi’u Sanusi Kano

An bukaci zababben gwamnan jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya kara kaimi wajen samar ma daliban da mai girma sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tura karatu da bayan kammalawar su basu samu aiki ba a jihar Kano.

Batun na zuwa ne daga bakin daya daga cikin makusanta zababben gwamnan na yanzu Hon Muftahu AG Abdullahi a wata zantawa da manema labarai a ranar talatar nan da ta gabata.

AG yace abu na farko shi ne godiya ga Allah bisa nasarar da jam’iyyar NNPP at samu na cin nasarar zaben Gwamna a Kano.

DG,AG yakara bayyana cewa babu shakka injiniya Abba Kabir zai yi tsayin daka wajen dorawa akan ayyukan da sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya aiwatar lokacin da yake gwamnan Kano, musamman tallafawa ‘Ya Yan talakawa zuwa karatu a kasashen waje, tallafawa mata da matasa da sana’o’i da kuma jari.

” Insha Allah Daga ranar da aka rantsar da injiya Abba Kabir Yusif a matsayin Gwamnan Kano ,jama’a zasu ga canji, musamman ta Fannin inganta cigaban ilmi, lafiya, aikin gona da samar da tsaftaccen Rowan sha ga alummar jihad Kano.”

Ya ce in sha Allahu alummar Kano za su samu cikakken nasara domin gwamnatin Abba Gida-Gida za ta inganta walwalar alummar Kano,inda ya kara da cewar sai an sami kwanciyar Hankali ne sannan rayuwa take inganta.

Jigon a tafiyar Gidan Abba Gida Gidan Honorable Abdullahi AG Abdullahi ya kuma baiwa alummar Kano tabbacin samun nagartattun ayyuka na raya kasa karkashin gwamnatin NNPP inda ya ce Abba Kabir Jan gwarzo ne, wanda yayi an gani a baya, musamman lokacin da ya rike mukamin kwamishinan ayyuka a jihar Kano.

Daga karshe AG ya bukaci al’ummar jihar kano da su cigaba da taya sabon gwamnan addu’o’in samun nasara a wannan lokaci dan cigaba gudanar da aikin alkhairi gare su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: