Muna Bukatar Sabuwar Gwamanati Ta Kula da Fannin Lafiya da Tattalin Arzikin Najeriya – Kachallah
Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna
Honarabul Madu Tela Kachallah, shine Kodineta na Kungiyar Magoya bayan Zabebben Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, wato Tinubu Support Movement (TSM), reshen Jihar Borno ya bayyana cewa suna bukatar Gwamanati Mai jiran gado da ta Kula da Fanin Lafiya da Tattalin Arziki kasancewar sa abune Mai mutukar mahimmanci a kowace Al’umma.
Ga dai yarda tattaunawar ta kasance kamar haka
Tambaya : Wani hali fannin lafiya ke ciki ne yanzu haka?
Madu Tela Kachallah: Abinda muke so shine, muna kira ga sabuwar Gwamanati da zata karbi Mulki nan bada dadewaba, da ta Kula da fannin lafiya da Tattalin Arzikin kasan nan.
Madu Tela : Kamar fanin lafiya, muna da bukatar Gwamanati mai zuwa da ta kula da Asibitoci tun daga Kananan hukumomi 774 da muke dashi a kasar nan, har zuwa gundumomi da a ingantasu. Haka kuma Inda babu to a Gina sabbi, kasancewar lafiya nada Muhimmanchi a ko wace Al’umma, kaga yanzun muna da mataimakin Shugaban Kasa, (vice president Elect) a Borno state Kuma mun San yanayin aikin da yayi, Gwamna shekara(8)toh yanzu muna Neman taimako a state din na matakin kasa wato (National level) gaba daya game da lafiya gaskiya akwai Chutar Koda, wannan Jihar Borno gaba daya tana fama da chutar Koda, haka lta kowani state a Nigeria tana fama da ita kowani jiha tana fama da lta,musamman kamar mu yan Borno ko me yake faruwa bamu Sani ba.
Madu Kachallah : Ba unguwan da zaka je basu da damuwar kidney problem Koda kenan to shin kowa ya san damuwar( kidney problem) Koda wannan ldan ya kama Mutum shan magani wahalan da ake sha da duniya gaba daya sai hankalinsu ya tashi kafin wanda Allah zai taimaka ya tashi Kuma yawanci dai Kashi 80% ba tashi suke yi ba to mun rasa Ruwan namu da muke sha ne ko abinci ne ko miye ne a Borno dai yafi yawa a game da duk Najeriya, shiyasa muke rokon Gwamanati da zai kama gaba ya kawo hankalinsa zuwa wajen, yayi bincike(Research) ya duba mana meye ne yake kawo wannan abun sai muyi kokari mu hadu da shi duka muyi maganin abun mu magance wannan abun shine damuwar mu a lafiya kenan.
Tambaya : Wani hali fanin bangeren tattalin Arziki ke ciki ne a Jihar Ku?
Amsa Madu Tela Kachallah : bangaran tattalin arziki Kuma shi damamatsan nan namu shine (youths) wannan shine concern, wato abin damuwa kenan, Kuma suna zaman banza, wasu na shaye-shaye, wan nan abu duk rashin aikin yi ne, saboda haka muna rokon Gwamanati da zata kama aiki zuwa gaba muna da mai a kasannan dan rashin zaman lafiya ne yasa aka bar maganan tonan mai.
Amma yanzu mun samu lafiya a jiharmu Gwamnan mu ya tashi tsaye an samu zaman lafiya wan nan, toh muna rokon Gwamanati me zuwa gaba shi Kuma ya taimaka ya je ya gyara mana hanyan mai wan nan,mai wannan in muka samu a Borno in sha Allahu kashi 60% na Matasa, (youths) zasu samu aiki a karkashinsu, Kuma kamfaninnika muna son Gwamanati muna da kamfaninnika tsofaffi da yawa a Borno wanda zan iya lissafawa kamfanin kwano, kamfanin kusa, kamfanin da ka sani wannan a Borno su kamfanin fulawa, kamfanin Alabo, ba abunda dai babu amma duka kamfanin sun mutu, kuma Jiha bazata lta farfado da suba, abin yafi karfinsu.
Saboda haka muna rokon Gwamanati da zata Karbi Mulki da ta tallafawa Kamfanonin nan su farfado, su tabbata an daga kamfaninnika nan ba kamfanin da a Borno da ba zai lya dauka Mutane ba aiki,akalla daga mutum zuwa 3000,5000,6000,9000. suna aiki amma yanzu haka duk an kulle yanzu an tsaya matasanmu yanzu in ba shaye-shaye da sata ba abunda suke yi Kuma rashin aikin shi yake kawo haka yau da gobe baka da aiki wannan dole ne kaje ka sata, kayi wani abu shiyasa.
Muna Neman Gwamanati yazo ya taimaka mana ya bude mana kamfaninnika nan,kuma Su hako manfetur din mu, in Allah ya yar da an gyara Kashi 80% na matasan gari zasu daina shaye-shaye, zasu daina sata, zasu daina zaman banza, zasu shiga aiki Kuma na tabbata matasa zasu goya wa Gwamnati baya.