Motoci da Buhari ya Bai wa Nijar ya Harzuƙa Wasu ‘Y an Najeriya

Daga BBC Hausa

Zafafan martani da shaguɓe iri-iri na ci gaba da biyo bayan matakin gwamnatin Najeriya na tallafa wa maƙwabciyarta Nijar da motocin da suka kai darajar kusan naira biliyan ɗaya da rabi.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ce ta bai wa maƙwabciyar tata motocin 10 da zimmar inganta ayyukan tsaro ne.

Hakan na zuwa ne a lokacin da Najeriyar ke tsaka da nata matsalolin tsaron a kusan kowane saƙo.

Ministar Kuɗi ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed, ta faɗa wa manema labarai ranar Laraba cewa “an ɗauki matakin ne saboda taimaka wa Nijar ta inganta tsaron iyakarta da Najeriya”.

Ƙasashen biyu da kuma Kamaru da Chadi, sun haɗa iyaka a tsakaninsu mai girma sosai kuma dukkansu na fuskantar hare-haren ƙungiyar Boko Haram da sauran masu iƙirarin jihadi.

A cewar ministar: “An ɗauki lokaci Najeriya tana tallafa wa makwabtanta, musamman ma mafiya kusanci da nufin karfafa su domin su kare kasashensu ta bangaren da ka iya shafar mu.

“Kuma ba wannan ne karon farko da Najeriya ta taimaka wa Nijar ko Kamaru ko Chadi ba.”

Binciken da BBC Hausa ta gudanar ya nuna cewa ba wannan ne karon ne Najeriya ta fara taimaka wa maƙwabtan nata ba kamar yadda Minista Zainab ta faɗa, amma a yanzu ne abin ya fi fitowa fili.

Sanata Shehu Sani ya wallafa cewa: “Abin tambayar shi ne, yaya aka yi ƴan majalisa ba su san da batun sayen motocin ba.”

Wasu takardun bayanai da wani ɗan jarida ya wallafa a ranar Laraba na sayen motocin sun tayar da ƙura, inda wasu ‘yan Najeriya ke tambayar me ya sa gwamnati za ta yi hakan alhalin ita ma tana da nata matsalolin.

Kazalika, ‘yan ƙasar da dama sun yi ta kwatanta ayyukan gwamnatin da kuma matsalolin, ciki har da waɗanda ke alaƙanta matakin rundunar sojan Najeriya na girmama dakarunta huɗu da sabbin babura “bisa jajircewarsu a wurin aiki”.

“An bai wa jajirtattun dakarunmu babura, an bai wa Nijar motoci ƙirar 2022,” a cewar ɗan jarida Abiodun Alade.

Kwamandan Bataliya ta 82 na Sojojin Najeriya a Jihar Enugu, Taoreed Lagbaja, ya karrama sojojin ne don ƙarfafa musu gwiwa tare ba su wasiƙun yabo a ranar Talata.

Haka nan, wasu na sukar gwamnatin saboda kasa daidaitawa da malaman jami’a, abin da ya sa suke yajin aiki na tsawon fiye da wata biyar ya zuwa yanzu.

Sai dai jami’an gwamnatin na kare matakin da cewa “idan da aka wani abu da za mu samu daga bai wa Nijar kyautar motoci shi ne wannan,” kamar yadda Tolu Ogunlesi ya bayyana yana mai nuni da wani kan labari da ke cewa Najeriya da Nijar da Aljeriya na shirin gina bututun iskar gas zuwa Turai.

Nijar ta karrama gwamnoni da attajiran Najeriya

Yayin da maƙwabtaka tsakanin Nijar da Najeriya ke ci gaba da yauƙaƙa kuma ake cecekuce, wasu gwamnoni da attajiran Najeriyar sun samu lambobin girmamawa a Nijar.

Shugaban Nijar Mohamed Bazoum ne ya karrama mutum shida da lambar yabo kan tsaro a bikin cikar ƙasar shekara 62 da samun ‘yancin kai da aka gudanar a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta.

Wadanda aka karrama sun haɗa da Gwamna Badaru Abubakar na Jigawa, da Gwamna Bello Matawalle na Zamfara, da hamshaƙan attajirai Aliko Dangote da Abdulsamad Rabi’u.

Sauran su ne Ambasada Lawal Kazaure da kuma Malam Sarki Abba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: