Mazauna Enugu Sun Ƙi Bin Umarnin Gwamnan Jihar Sun Zauna A Gida


Daga BBC

Mazauna birnin Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya sun yi watsi da umarnin da gwamnan jihar ya bayar na bijire wa umarnin ƙungiyar IPOB na zaman gida a ranar Litinin a jihar.


Rahotonni sun ce tituna da makarantu da bankuna da kasuwanni da sauran wuraren gwamnati ke ci gaba da kasancewa babu mutane.


A ranar 1 ga watan Yuni ne gwamnan jihar Peter Mbah ya yi iƙirarin cewa daga yanzu ya haramta batun zama a gida da ƙungiyar IPOB ta bayar.


Yana mai kira ga al’umma da ɗaiɗaikun ƙungiyoyi a faɗin jihar su fita harkokinsu na yau-da-kullum.


Mista Mbah ya ce gwamnatinsa a shirye take ta tattauna da mutanen da ke da kyayyawar aniyar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali domin tabbatar da tsaro da zaman lafiyar jihar.


Kungiyar IPOB ta kwashe watanni tana saka dokar zaman gida a wasu ranaku a yankin kudu maso gabashin Najeriya.


Matakin da masana tsaro ke kallo a matsayin babbar barazana ga tsaron ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: